Jami'an Tsaro Sun Mamaye Sakateriyar Jam'iyyar PDP a Jihar Ondo

Jami'an Tsaro Sun Mamaye Sakateriyar Jam'iyyar PDP a Jihar Ondo

  • Jami'an tsaro sun kwace iko da babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP da ke Akure babban birnin jihar Ondo da safiyar ranar Litinin
  • Rahoto ya nuna cewa yan sanda da DSS sun kewaye babbar ƙofar shiga yayin da matasan PDP ke shirin fara zanga-zamga
  • Mambobin PDP sun ce zasu yi zanga-zanga ne domin a fito a bayyana wa al'umma inda gwamna Akeredolu ya koma da zama

Jihar Ondo - Jami'an hukumomin tsaro sun mamaye babbar Sakatariyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke Akure, babban birnin jihar Ondo.

Jaridar Punch ta tattaro cewa an girke jami'an tsaro ta ko ina a Sakateriyar, wanda suka haɗa da dakarun rundunar 'yan sanda da jami'an farin kaya (DSS).

Jami'an tsaro a jihar Ondo.
Jami'an Tsaro Sun Mamaye Sakateriyar Jam'iyyar PDP a Jihar Ondo Hoto: Oyeniran Boluwaji
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa an ga jami'an tsaron sun girke motocinsu a ƙofar shiga sakateriyar PDP tun da sanyin safiyar ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Sanda Suka Kama Fasto da Wasu Mutum 3 da Kokon Kan Dan Adam, Sun Fadi Abin da Za Su Yi da Shi

Bisa la'akari da yuwuwar cin mutunci da tsangwama, shugabannin jam'iyyar ba su fita aiki ofisoshinsu ba domin guje wa abin da ka iya zuwa ya dawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa jami'an tsaro suka ɗauki wannan matakin?

An tattaro cewa tura tulin jami'an 'yan sanda wurin ba zai rasa nasaba da shirin zanga-zangar da matasan jam'iyyar PDP suka kudiri aniyar yi ba.

Matasan PDP a jihar sun lashi takobin tsunduma zanga-zangar luma yau Litinin saboda rashin ganin gwamna Rotimi Akeredolu a jihar.

Mambobin PDP sun shirya yin wannan zanga-zanga domin nuna adawa da rashin zuwa ofis din da gwamna, Rotimi Akeredolu, ke yi da kuma zargin ba a san inda ya shiga ba.

Gwamna Akeredolu ya sha jinya a Jamus

A watan Satumba ne Akeredolu ya dawo kasar daga hutun jinya na watanni uku a Jamus inda ya yi jinyar rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Shugaban 'yan sanda zai tafi turai taron da zai sauya lamarin tsaron Najeriya

Amma tun bayan dawowarsa, Gwamnan ya koma gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo da zama, lamarin da ya haddasa cece-kuce da sukar gwamnatinsa.

A ranar Lahadi ne babbar jam’iyyar adawa PDP ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga a Akure, domin neman a bayyana inda gwamnan ya shiga.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu jin ta bakin kakakin 'yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya ba, in ji rahoton Daily Trust.

"Ba Mu Dakatar da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna Ba" Majalisar Ondo

A wani rahoton kuma Kujerar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, na kan siraɗi mai wahala har yanzu dangane da batun tsige shi.

Majalisar dokokin jihar Ondo ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262