Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Kada Ta Karbi Sabbin Hujjojin Atiku

Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Kada Ta Karbi Sabbin Hujjojin Atiku

  • Ana cigaba da fafatawa tsakanin ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar da shugaban ƙasa Bola Tinubu a kotun ƙoli
  • Yayin da Tinubu ya bukaci kotun da ta yi watsi da ƙarar Atiku da PDP saboda rashin cancanta, Atiku ya buƙaci kotun ƙoli da ta kori shugaban ƙasar
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci kotun ƙolin ka da ta karɓi sabbin shaidun da Atiku ya kawo saboda bai gabatar da su tun da farko ba

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa a halin yanzu kotun koli ba za ta iya karɓar sabbin hujjojin da Atiku Abubakar ya nema ya gabatar a ƙararrakin da ya shigar a gabanta ba.

Atiku ya garzaya kotun ƙoli yana ƙalubalantar sakamakon zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Tinubu ya bukaci kotun koli ka da ta karbi hujjojin Atiku
Tinubu ya bukaci kotun koli kada ta amshi sabbin hujjojin Atiku Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Meyasa Tinubu bai son a karɓi hujjojin?

Shugaban na Najeriya ya buƙaci kotun ƙolin ta yi watsi da sabbin hujjojin da Atiku da jam’iyyarsa ta PDP suka gabatar na cewa sun samo daga jami'ar jihar Chicago (CSU), cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya gamsu da cewa kotun ƙoli ba za ta iya sake ɗaukar hurumin shari'a a ƙarar ba tunda kwanaki 180 na sauraron ƙararrakin zaɓen sun ƙare.

Ya ƙara da cewa, ba wai kawai sabbin shaidun abin mamaki ba ne, amma Atiku da PDP waɗanda suka kasance masu shigar da ƙara a kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban kasa (PEPC), ba su ƙalubalanci sakamakon zaɓen kan dalilin yin amfani da jabun takardu ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ya ƙalubalanci Atiku da PDP

A wani mataki makamancin haka, shugaban masu rinjyae na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya dage cewa Atiku da PDP ba su taɓa roƙon kotu cewa za su kawo wata takarda daga CSU ba, domin goyon bayan ƙorafinsu na huɗu na rashin cancantar Tinubu.

Kara karanta wannan

An Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sanya Wike Ya Gana da Bukola Saraki

Tinubu da Bamidele sun bayyana hakan ne a lokacin da suke mayar da martani ga buƙatar Atiku da jam’iyyarsa ta neman izinin kotun koli na gabatar da sabbin shaidu a ɗaukaka ƙarar da suka shigar.

An Shawarci Tinubu Kan Atiku

A wani labarin kuma, wata ƙungiya ta shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya tumɓuke karramar GCON da Atiku Abubakar yake da ita.

Ƙungiyar wacce ke fafutukar ganin an gudanar da shugabanci nagari a Najeriya, ta yi wannan kiran ne biya bayan matsin lambar da Atiku ya yi wa Tinubu kan takardun karatunsa na CSU.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng