An bayyana Dalilin da Yasa Wike Da Saraki Suka Sanya Labule
- Nyesom Wike, Saraki, Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal sun yi takarar shugaban ƙasa a 2023 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP
- Atiku ya yi nasara a kansu inda ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a babban zaɓen 2023
- Sai dai, batun karɓa-karɓa ya haifar da ruɗani a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar PDP yayin da ƴan siyasar Kudancin ƙasar suka dage cewa sai shugabancin jam'iyyar ya koma yankin
FCT, Abuja - An bayyana ainihin dalilin da yasa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT) da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, suka sabunta alaƙarsu a cikin ƴan kwanakin nan.
Jaridar The Punch ta gano dalilin da ya sa tsohon gwamnan jihar Rivers da Saraki suka ziyarci juna ba ya rasa nasaba da batun samo wanda zai shugabanci jam'iyyar PDP na ƙasa.
Ku tuna cewa Saraki da Wike a watan Mayun 2022, sun fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP, amma sun sha kaye a hannun, Atiku Abubakar wanda ya zama dan takarar jam’iyyar bayan ya samu kuri'u 371.
Meyasa Wike ya gana da Saraki?
Wata majiya mai tushe wanda mamba ne kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na PDP, ya bayyana wa jaridar cewa batun wanda zai gaji Damagum na daga cikin dalilin da ya sa Wike ya ziyarci Saraki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya a jam'iyyar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa Atiku da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun amince da Saraki ya gaji Damagum.
A kalamansa:
"Muna sane da cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Atiku, da wasu jiga-jigan jam’iyyar suna tattaunawa kan mutumin da zai gaji Damagum. A ƴan kwanakin nan, na san Atiku da wasu daga cikin shugabannin sun amince da Saraki."
"Sun amince da Saraki ne saboda sun yi amanna cewa yana da kwarjini da kuma manufar siyasa domin sake farfaɗo da jam'iyyar. Domin haka ana cigaba da tattaunawa a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar."
Sai dai majiyar ta kammala da cewa shari'ar Atiku da PDP da ke gaban kotun koli ita ce ke kawo jinkiri wajen bayyana sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Gwamna Yahaya Zai Biya Yan Fansho Bashi
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Gombe zai biya bashin ƴan fansho da masu gratuti su ka biyo jihar.
Gwamna Inuwa Yahaya zai biya bashin kuɗaɗen da ƴan fanshon suke bi da kuɗaɗen da ya ƙwato a hannun tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Dankwambo.
Asali: Legit.ng