"Ba Mu Dakatar da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna Ba" Majalisar Ondo
- Kujerar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, na kan siraɗi mai wahala har yanzu dangane da batun tsige shi
- Majalisar dokokin jihar ta musanta rahotanni da ke yawo cewa ta dakatar da shirin sauke mataimakin gwamna daga kan kujerarsa
- Ta ce a halin da ake ciki Alkalin Alƙalan jihar ya gaza kafa kwamiti ne saboda umarnin Kotu amma tana kan warware matsalar
Jihar Ondo - Majalisar dokokin jihar Ondo ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.
Channels tv ta tattaro cewa yayin da majalisar dokokin ke musanta jita-jitar, ta ayyana rahotannin da ake yaɗa wa da, "wasu gurɓatattun labarai," da ba su da tushe.
Majalisar ta bayyana cewa ba gudu ba ja da baya, zata ci gaba da bin matakan tsige mataimakin gwamnan har sai ta kai ƙarshe kamar yadda doka ta tanada.
A cewarta, sai ta kai ƙarshe ne sannan zata tabbatar da gaskiya kan manyan zarge-zargen da aka rataya wa mataimakin gwamnan na rashin ɗa'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan bayani na ƙunshe ne a wata sanarwa da lauyan majalisar jihar Ondo, Femi Emodamori, ya rattaba wa hannu ranar Asabar.
Ina aka kwana kan shirin sauke mataimakin gwamna?
Majalisar Ondo ta yi nuni da cewa ta bi duk matakan da suka dace kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada har zuwa matakin da ake bukatar babban alkalin jiha ya kafa kwamitin mutum 7.
Wannan kwamitin ne zai bincike da nazarin kan tuhume-tuhumen da ake wa mataimakin gwamnan kana ya miƙa rahoton abin da ya gano, The Cable ta ruwaito.
Ta ce bayan umartan shugaban alkalan jihar ya kafa wannan kwamiti, sai ya dawo mata da amsar cewa Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi umarnin kar ya kafa kwamitin.
A cewar majalisar, ta fara koƙarin soke umarnin Kotun da korar ƙarar da mataimakin gwamnan ya shigar gaba ɗaya domin ta ba Alkalin alƙalai damar yin abinda ya dace.
Gwamnatin Borno Ta Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai a Fadin Jihar
A wani rahoton na daban Gwamnatin Borno karƙashin Gwamna Babagana Zulum ta haramta aikin haƙar ma'adai a faɗin jihar da nufin dawo da zaman lafiya.
Kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar, ya gargaɗi ma'aikata su kiyaye wannan haramcin ko doka ta hau kansu.
Asali: Legit.ng