Zaben Kogi: "Ma Tsallake Harin Ƙisa Har Sau Hudu" Sanata Dino Melaye
- Sanata Dino Melaye ya yi iƙirarin cewa sau huɗu ana yunƙurin kashe shi yana tsallake wa da ƙyar a jihar Kogi
- Melaye, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben jihar mai zuwa, ya ce tun da APC ta hau mulki tashin hankali ya zama ruwan dare
- Ya ce idan PDP ta karɓi mulki a zaɓen 11 ga watan Nuwamba, zata fara haɗa kan mutane wuri ɗaya
Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya a harin kisan da aka kai masa.
Sanata Melaye ya yi wannan furucin ne a wata hira da Arise TV ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023.
A cewarsa, tun da aka wayi gari APC ta karbi ragamar mulkin jihar Kogi shekaru bakwai da rabi da suka wuce, rashin zaman lafiya ya zama ruwan dare har mutane sun saba.
A rahoton Vanguard, ɗan takarar PDP, Melaye ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na tsallake rijiya da baya sau huɗu yayin da aka yi yunƙurin kashe ni, akwai ƙararraki 12 a Kotu wanda gwamnatin tarayya ke fafatawa da Dino. An kai mun hari da dama."
"Ba sabon abu bane wannan domin al'adar APC kenan, abin da suke so kar a zauna lafiya. Jihar nan tamu Kogi ta zama abin tsoro kamar mugun jeji wan da ke bukatar sake ginawa nan take."
Zamu ceto Kogi mu sake gina ta - Melaye
Melaye, ɗaya daga cikin na hannun daman Atiku Abubakar, ya ce yana fatan ya bada gudummuwa iyakar iyawarsa domin ceto jihar da yaye wa jama'a halin da suka shiga.
A cewarsa, komai ya lalace a jihar Kogi tunda APC ta ɗare mulki, ta raba kawunan al'umma ta yadda al'amura suka caɓe wanda ba a taba samun irin haka ba a tarihi.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2
Ɗan takarar ya ƙara da cewa ajandojin PDP sun ƙunshi a fara hada kan jihar, domin taken yakin neman zabensa shi ne, “Kogi daya, makoma daya.”
Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa
A wani rahoton mun kawo muku cewa Jam'iyyar APC ta ɗage gangamin kaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a zaben Baylesa.
Kakakin APC, Felix Morka, ya ce an ɗage kaddamar da kamfen daga.ranar Asabar, za a sanar da sabuwar rana nan gaba.
Asali: Legit.ng