Sokoto: Ko Kwandala Ban Taras a Baitul Mali Ba, Gwamna Ahmad Aliyu

Sokoto: Ko Kwandala Ban Taras a Baitul Mali Ba, Gwamna Ahmad Aliyu

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya yi ikirarin cewa tsohon gwamna, Aminu Tambuwal bai bar masa ko kwandala ba a baitul-malin jihar Sakkwato
  • Aliyu ya bayyana irin sadaukarwan da gwamnatinsa ta yi har ta cimma nasarar aiwatar dumbin ayyuka a cikin kwana 100 na farko
  • Ya faɗi haka ne yayin da mataimakin kakakin majalisar wakilai ya jagoranci tawaga suka je ta'aziyyar rasuwar abokin aikinsu

Jihar Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ce ya gaji baitul mali babu ko sisi kuma ko takardar Naira daya tsohon gwamna, Aminu Tambuwal, bai mika masa ba.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya amsa tambayar mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kanu, ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu.
Sokoto: Ko Kwandala Ban Taras a Baitul Mali Ba, Gwamna Ahmad Aliyu Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yayin zaiyarar ta'aziyya da ya je Sokoto, Kanu ya tambayi gwamnan taya ya iya aiwatar da ayyuka 100 cikin kwanaki 100 da hawa mulki.

Kara karanta wannan

Jihohin PDP da APC 4 da Ake Zaman 'Doya Da Manja' Tsakanin Gwamna da Mataimaki

Aliyu wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa, Idris Gobir, ya ce sadaukarwa ce kawai domin babu ko kwandala a baitul mali sa'ilin da ya karbi ragamar mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

“Mun gaji Baitul-mali babu ko kwandala, ba abin da za mu iya nunawa, babu takarda ko daya da aka mika mana."
"Mun sadaukar da kanmu domin sauya akalar jihar nan kuma mun samu nasarar kawo canji a kwanaki 100 na farko."

Ya bayyana dangantakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da majalisa a matsayin mai kyau, inda ya ce jagoran APC na Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya kimtsa su.

Gwamna ya miƙa godiya ga tawagar majalisar wakilai

Aliyu, ya mika godiya ga jagororin majalisa bisa turo tawaga domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan rasuwar abokin aikinsu kuma mamba mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni, Jelani Danbuga.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Gwamnan ya kuma bayyana marigayi dan majalisar a matsayin mai kishin kasa kuma cikakken mutum na gari.

Abin da ya kawo mu jihar Sakkwato - Kanu

Tun da farko, mataimakin kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Kanu ya ce sun ji dadin irin ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar zuwa yanzu.

A cewarsa, abin farin ciki ne ganin yadda shugabanci a matakin jiha ke yin tasiri mai kyau ga rayuwar al’umma.

Ya bayyana cewa sun zo Sokoto ne domin jajanta wa al’ummar jihar bisa rasuwar abokin aikinsu wanda ya yi imani da hadin kai da ci gaban kasa.

"Ka Daina Amince Wa da Kudirori Ba Tare da Sanin Mu Ba" Sanatoci Ga Akpabio

A wani rahoton na daban kuma Sanatoci sun fara yi wa shugaban majalisar dattawa bore kan zartar da kudirori ba tare da saninsu ba.

Sanata Ali Ndume ya caccaki Godswill Akpabio kan amince wa da kudirori ba tare da karanta su a gaban sauran mambobin majalisa ba.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Ya Bai Wa Matashin Da Ya Dawo Da N15m Yayin Aikin Hajji Kujerar Makka, Aiki, Ya Masa Goma Ta Arziki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262