Jigon Jam'iyyar Labour Ya Bayyana Yadda Obasanjo Ya Dakeshi a Gidansa Don Ya Tona Asiri

Jigon Jam'iyyar Labour Ya Bayyana Yadda Obasanjo Ya Dakeshi a Gidansa Don Ya Tona Asiri

  • Abayomi Arabambi, kakakin jam'iyyar Labour ya bayyana cewa Obasanjo da shugaban Afenifere su ne silar rikicin jam'iyyar
  • Abayomi ya ce Obasanjo ya mishi dukan tsiya kan tona asirin cewa Abure ya kwafi sa hannun babbar kotun Tarayya
  • Ya ce Obasanjo da Peter Obi sun bukaci a bar maganar har sai sun ci zabe kafin daga baya a shawo kan matsalar

FCT, Abuja - Kakakin tsagin jam'iyyar Labour, Abayomi Arabambi ya zargi tsohon shugaban kasa, Obasanjo da dukanshi a gidansa.

Arabambi ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na AIT a jiya Alhamis 12 ga watan Oktoba.tattaro.

Jigon jam'iyyar Labour ya bayyana dalilin da ya sa ya sha dukan tsiya a hannun Obasanjo a gidansa
Jigon Jam'iyyar Labour ya yi martani kan dalilin rikicin jam'iyyar. Hoto: Olusegun Obasanjo, Abayomi Arabambi.
Asali: Twitter

Meye ake zargin Obasanjo kan rikicin jam'iyyar Labour?

Abayomi ya ce Obasanjo ya dake shi ne kan zargin badakalar takardu da ake yi wa shugabannin jam'iyyar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Dambarwar Satifiket: ‘Peter Obi Zai Ci Amanar Najeriya Kamar Yadda Ya Yi Wa Ojukwu’, Jigon APC Ya Yi Zargi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon Labour ya ce ya bayyana wa Obasanjo da Ayo Adebanjo cewa Julius Abure ya kwafi sa hannun babbar kotun Tarayya.

Arabambi ya ce wannan shi ne silas rikicin jam'iyyar inda aka umarce shi da ya yi shiru don kawai Peter Obi ya ci zabe.

Ku kalli hirar a kasa:

Meye Abayomi ke cewa kan Obasanjo?

Ya ce lokacin da Obi da sauran manyan jam'iyyar su ka samu labarin almundahana na Abure sai su ka ce a bari Obi ya ci zabe idan ya so sai shawo kan maganar daga baya.

Ya ce:

"Obasanjo ya sani, Adebanjo shi ma ya sani dole na fadi gaskiya yanzu, shi ne dalilin da ya sa Obasanjo ya dake ni a gidansa.
"Mun bayyana musu almundahana da aka yi a kotu amma su ka ce mu bari tukun Obi ya ci zabe, mu kuma mu ka ce ba za mu yarda ba.

Kara karanta wannan

Abin Takaici Yayin da Lauyoyi Su Ka Doku da Jifa da Kujeru a Cikin Kotu, Bidiyon Ya Jawo Cece-kuce

Peter Obi ya yi fatali da bukatar hadin kai na Atiku

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ki amincewa da bukatar Atiku Abubakar na hada kai don kwato mulki a hannun Tinubu.

Obi ya ce shi ma ta kansa ya ke yi don haka kowa ya ji da kansa wurin neman hakkinsa.

Obi da Atiku na kalubalantar zaben Tinubu da su ke zargin an tafka kura-kurai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel