Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Karar Da Atiku Ya Daukaka

Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Karar Da Atiku Ya Daukaka

  • An buƙaci kotun koli ta yi watsi da ƙarar da Atiku na jam'iyyar PDP, ya shigar kan hukuncin kotun da ta tabbatar da zaben shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Tinubu ya ce ƙarar da Atiku ya shigar ba ta da wani inganci kuma hakan na nuni ne da yadda ake cin zarafin harkokin kotu
  • Shugaban ƙasan ya buƙaci kotun kolin ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta yanke

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kotun koli ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen da ya gudana na ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ranar 18 ga watan Satumba ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar da jam'iyyar PDP suka shigar da ƙara a gaban kotun inda suka buƙaci kotun kolin ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta yanke, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon APC Ya Bukaci a Kori Tinubu Daga Shugabancin ECOWAS, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Tinubu ya bukaci kotun koli ta kori karar Atiku
Shugaba Tinubu na son kotun koli ta yi fatali da karar da Atiku ya daukaka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya bayar da hujjar cewa hukuncin da kotun ta yanke na rashin adalci ne kuma cike yake da kurakurai da rashin fayyace gaskiya.

Da yake mayar da martani kan ƙarar da Atiku ya shigar, Tinubu ya buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar saboda "cin zarafi ce", a cewar rahoton TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Tinubu yake son a kori ƙarar?

Shugaban ya ce kotun zaɓen ta yi daidai wajen tabbatar da nasararsa domin Atiku da PDP sun kasa tabbatar da dukkanin zarge-zargen da suka gabatar.

"Babu ko ɗaya daga cikin masu shigar da ƙarar da suka ba da dalilin da zai sanya wannan kotun mai girma ta yi katsalandan kan hukuncin da karamar kotun ta yanke wand akaa yanke bisa bin tanadin doka." A cewarsa
“Saboda haka muna kira ga wannan kotu mai girma da ta tabbatar da hukuncin da karamar kotun ta yanke, tare da yin watsi da wannan daukaka ƙarar gaba ɗayanta, domin bata da inganci da rashin cancanta."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Batun Tsige Mataimakin Gwamnan APC

Tinubu Ya Ba Yaron Aminin Buhari Mukami

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaƙulo yaron aminin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ba shi muƙami.

Shugaban ƙasar ya naɗa Dr. Aminu Maida a matsayin sabon shugaban hukumar NCC wacce ke kula da harkokin sadarwa a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng