Jerin Bayanan Takardun Karatun da Tinubu, Atiku, Peter Obi, Kwankwaso Suka Ba INEC Kafin Zaben 2023
Biyo bayan zargin yin amfani da takardun jabu, da aka yi kan Shugaba Tinubu, da samun takardun bayanan karatun shugaban ƙasar da Atiku Abubakar ya yi, bayanai sun fito kan takardun da ƴan takarar suka ba hukumar INEC.
Hakan na zuwa ne bayan an ƙwaƙulo bayanan karatun Atiku, Tinubu, Rabiu Kwankwaso na Jam’iyyun New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Peter Obi na Jam’iyyar Labour (LP) da suka miƙa wa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) gabanin 2023.
Bola Tinubu
A cikin rahoton da Premium Times ta wallafa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sana'arsa ita ce 'siyasa' kuma ya samu digiri a fannin kasuwanci da gudanarwa a jami'ar jihar Chicago a ranar 22 ga Yunin 1979.
Shugaba Tinubu ya zarce zuwa wajen yi wa ƙasa hidima a shekarar 1982.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya kuma gabatar da shaidar rantsuwa cewa ya rasa takardunsa bayan wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun kai hari a gidansa.
Atiku Abubakar
Shi ma Atiku Abubakar akwai alamar tambaya a kan shaidar takardun kammala karatunsa, waɗanda ya miƙa wa hukumar zaɓe ta INEC.
Kamar Tinubu, Atiku shi ma bai bayar da bayanai kan karatunsa na firamare ba.
Takardar shaidar zana jarabawar kammala karatun sakandare ta African Senior Secondary School Certificate (WASSSC) ta shekarar 1965 da ya ba INEC ɗauke take da sunan Siddiq Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi iƙirarin cewa yana da digirin digirgir a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa daga jami'ar Anglia Ruskin da ke ƙasar Birtaniya ba tare da bayar da bayanai kan sauran digirinsa ba.
Rabiu Kwankwaso
Ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaben 2023, ya sha bamban da Atiku da Tinubu, domin ya bayar da bayanan karatunsa ga hukumar zaɓen.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya samu takardar shaidar kammala karatunsa na firamare a shekarar 1968, sannan ya samu shaidar kammala sakandare a shekarar 1975.
Kwankwaso ya gabatar da takardun shaidar karatunsa da suka hada da Craft Training Certificate, ND, HND, PGD, M.Sc da Ph.D.
Peter Obi
Ɗan takarar jam'iyyar Labour ya shiga takarar ne bayan ya fice daga jam’iyyar PDP kuma ya zama ɗan takarar da aka fi maganarsa a shafukan sada zumunta.
Kamar Tinubu, Obi ya bayyana kansa a matsayin dan siyasa a wajen sana'arsa. Ya shahara wajen faɗin alkaluma da ƙididdiga a kowace dama da aka ba shi.
Obi, wanda shi ne ɗan takara mafi ƙarancin shekaru a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya halarci makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu tsakanin 1973 zuwa 1984 bisa ga bayanan takardun karatunsa da ke hannun hukumar INEC.
Jam'iyyar Labour Party Ta Bayyana Dalili 1 Rak Da Ya Sa Peter Obi Ba Zai Yi Aiki Da Gwamnatin Tinubu Ba
Peter Obi Ya Magantu Kan Takardun Karatun Tinubu
A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi magana kan taƙaddamar da ake yi kan takardun karatun Shugaba Tinubu.
Peter Obi ya bayyana taƙaddamar a matsayin abun kunya ga Najeriya, inda ya buƙace shi da ya fito ya gayawa ƴan Najeriya gaskiya.
Asali: Legit.ng