Kashim Shettima da Gwamnonin APC Sama da 10 Sun Dira Jihar Imo

Kashim Shettima da Gwamnonin APC Sama da 10 Sun Dira Jihar Imo

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa jihar Imo domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen APC
  • Gwamna Hope Uzodinma da wasu gwamnonin APC ne suka je filin sauka da tashin jiragen sama suka tarbi Shettima
  • Uzodinma na fafutukar neman zarcewa a kan kujerar gwamna karo na biyu yayin da zai shiga zaɓe a matsayin ɗan takarar APC

Jihar Imo - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya domin kaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna na jam'iyyar APC.

Rahoton jaridar The Nation ya gano cewa tun da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar yau Laraba, 11 ga watan Oktoba, 2023 aka buɗe babbar ƙofar shiga babban filin wasan Dan Anyiam a Owerri.

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya isa Imo.
Kashim Shettima da Gwamnonin APC Sama da 10 Sun Dira Jihar Imo Hoto: Willy Ibimima Jim-george
Asali: Facebook

An ce an buɗe babban filin kwallon domin dubannin magoya bayan APC daga ƙananan hukumomin jihar Imo 24 su shiga, kuma tuni wurin ya cika ba masaka tsinke.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 Na Arewa Sun Gana a Katsina, Sun Cimma Matsaya Kan Muhimman Abu 2

Gwamnonin APC sama da 10 sun isa Imo

Bayanai sun nuna cewa gwamnonin APC 14 sun isa wurin taron, inda za a buɗe shafin yaƙin neman tazarcen gwamnan jihar, Hope Uzodinma, a zabe mai zuwa nan da wata ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin gwamnonin da aka hanga a Imo sun haɗa da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Biodun Oyebanji na jihar Ekiti, Francis Nwifuru na jihar Ebonyi da sauransu.

Gwamna Uzodinma na ƙoƙarin kare martabarsa ya zarce zango na biyu a kujerar gwamna a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

An yi hasashen cewa gwamnan, ɗan takara a inuwar jam'iyyar APC na da damar lashe zaɓen fiye da sauran 'yan takara.

Sai dai ana ganin duk da haka akwai jan aiki a gabansa duba da yadda manyan jam'iyyun adawa PDP da LP suka mamaye Kudu maso Gabas a zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Samu Mukami Mai Muhimmanci

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin na daban kuma Majalisar wakilai ta ƙasa ta ɗage zamanta sakamakon rasuwar ɗan majalisa daga jihar Sakkwato ranar Laraba.

Mamba mai wakiltar Isa da Sabon Birni, Abdulkadir Danbuga, ya rasu yana da shekara 63 a duniya bayan fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262