Ya Zama Wajibi Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ainihin Bayanansa, Peter Obi

Ya Zama Wajibi Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ainihin Bayanansa, Peter Obi

  • Peter Obi ya ce taƙaddama kan ainihin takardun bayanan Bola Tinubu abin kunya ne ga Najeriya a idon ƙasashen duniya
  • Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a zaɓen 2023 na LP ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya bayyana gaskiya kan haƙiƙanin bayanansa
  • Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce kamata ya yi shugaba Tinubu ya bayyana inda ya yi NYSC, shi ɗan wace ƙasa ne da takardun shaidarsa

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fito ya yi wa 'yan Najeriya jawabi kan haƙiƙanin bayanansa.

Obi ya ce bai kamata Tinubu ya bar mukarrabansa su riƙa yin bayani ba, yana mai cewa hatta kasashen duniya ma za su so sanin hakikanin waye shi, Vanguard ta rauwaito.

Kara karanta wannan

"Yadda Isra'ila Ke Kokarin Kitsa Yakin Duniya Na 3": Tsohon Minista Ya Bayyana Hadarin Da Ke Tafe

Peter Obi da shugaba Tinubu.
Ya Zama Wajibi Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ainihin Bayannasa, Peter Obi Hoto: Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar rahoton Leadership, Peter Obi ya yi wannan furucin ne a wurin taron 'yan jarida na duniya a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Da yake jawabi, Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce kamata ya yi shugaban ƙasa Tinubu ya ceci Najeriya daga wannan abin kunya kana ya fito ya bayyana ainihin shi waye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya kamata Tinubu cikin tawali’u da girmamawa ya fito ya bayyana haƙiƙanin bayanansa, duniya ta san sunanka, ƙasarka da takaddun shaida," in ji shi.

Abinda ya kama shugaba Tinubu ya yi

Obi ya roki shugaba Tinubu ya sake fadawa ‘yan Najeriya makarantun da ya halarta, da kuma lokacin da ya yi bautar kasa (NYSC) na shekara daya.

Ya kuma bukace shi da ya fayyace ko da gaske ne ya canza sunansa a kowane lokaci domin ceto kasar daga abin da ya kira abin kunya a idon kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ba Da Kariya Kan Rikicin Kasar Da Falasdinu, Ta Fadi Dalilai

Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa kasancewar yana zaune a kujera lamba ɗaya a kasar nan, shugaba Tinubu ba ya da wani hakki na sirri dangane da ainihin bayanansa.

Channels tv ta rahoto Obi na cewa:

“Ya kamata ka bayyana a fili inda ka yi NYSC. Idan ka taɓa canza suna ka yi bayani filla-filla, abin da ake buƙata Tinubu ya fito ya bayyana haƙiƙanin waye shi. Mutane na son sani."

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

A wani rahoton kuma Shugaba Tinubu ya tunanin kirkiro sabbin Kotuna na musamman da za a riƙa hukunta masu kashe mu raba da kuɗin baitul mali.

Irin wannan kotu na musamman za ta yi kokarin yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa a fadin Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262