Sylva Ya Daukaka Kara Kan Hukuncin da Kotun da Ta Soke Takararsa a Zaben Bayelsa
- Ɗan takarar gwamna a inuwar APC a zaben jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke
- Tsohon ministan ya musanta hana shi takara da alkalin Kotun ya yi, ya roƙi Kotun daukaƙa ƙara ta tabbatar masa da takararsa
- Kotun dai ta soke takarar Sylva na jam'iyyar APC bisa hujjar cewa sau biyu ana rantsar da shi a matsayin gwamnan Bayelsa
Bayelsa - Tsohon ƙaramin Ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya ɗaukaka ƙara dangane da hukuncin da babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke.
The Nation ta tattaro cewa Sylva ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin wanda ya soke tikitin takararsa ta gwamna a inuwa jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa.
Mai shari’a Okorowo, a hukuncin da ya yanke a yammacin ranar Litinin, ya kori Sylva bisa dalilin cewa an rantsar da shi sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan jihar Bayelsa.
Tsohon ministan ya ɗaukaka ƙara
A takardar daukaka kara da aka shigar a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, Sylva ya yi fatali da hukuncin wanda mai shari’a Donatus Okorowo ya yanke kuma ya bukaci kotun da ta ajiye shi a gefe kana ta tabbatar masa da takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma shigar da buƙatar cewa a jingine aiwatar da hukuncin babbar Kotun tarayya har sai Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar da ya shigar.
Jam'iyyar APC ta yi fatali da hukuncin Kotun
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, jam'iyyar APC reshen jihar Bayelsa ta ce ba ta yarda da hukuncin hana Sylva takara ba, inda ta sha alwashin ɗaukaka ƙara.
A cewar APC, baki ɗaya ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar a gaban Kotun ta saɓa wa kundin dokokin zaɓen Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Zaben Kogi: Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Kogi yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a wata mai zuwa.
Ɗan siyasan ya bayyana cewa ya yanke shawarar koma wa jam'iyyar AA ne domin tabbatar da daidaito, gaskiya da adalci a kujerar gwamnan jihar Kogi.
Asali: Legit.ng