Kotu Ta Kori Karar da Ta Nemi a Dakatar da Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Ondo
- Mataimakin gwamnan jihar Ondo da ke fuskantar barazanar tsige shi ya yi rashin nasara a babbar Kotun Akure
- A hukuncin da ta yanke kan ƙarar da ya shigar, Kotun ta ce ba ta hurumin kawo abin ka iya haddasa cin karo a ɓangaren shari'a
- Ta ce mataimakin gwamnan ya ci mutuncin shari'a saboda ya shigar da ƙara iri ɗaya a babbar Kotun tarayya da babbar Kotun Ondo
Jihar Ondo - Babbar Kotun jihar Ondo mai zama a Akure ta yi watsi da ƙarar da mataimakin gwamnan jihar, Honorabul Lucky Aiyedatiwa, ya shigar kan shirin tsige shi.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa mataimakin gwamnan ya shigar da ƙara gaban Kotun ne yana kalubalantar yunƙurin majalisar dokokin jihar na raba shi da kujerarsa.
Da yake yanke hukunci ranar Talata, mai shari'a O. Akintan-Osadebay, ya ce ba shi da hurumin yanke hukuncin da ka iya haddasa cin karo tsakanin babbar Kotun Ondo da babbar Kotun Abuja.
Alƙalin ya bayyana cewa hakan cin mutuncin shari'a ne duba da yadda ya shigar da ƙara iri ɗaya a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja da kuma babbar Kotun Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abinda ƙarar ta ƙunsa
Idan dai baku manta ba, Aiyedatiwa, ya garzaya kotun ya shigar da ƙara mai lamba AK/348/2023 ranar 25 ga watan Satumba, 2023, domin ta dakatar da majalisa daga tsige shi.
A ƙarar, Mista Aiyedatiwa ya roƙi Kotu ta bada umarnin hana majalisar dokokin jihar daga ci gaba da bin matakan sauke shi daga kujerar mataimakin gwamna.
Ya kuma nemi Kotu ta hana babban alkalin jihar daga bin umarnin majalisa na kafa kwamitin da zai binciki zargin rashin ɗa'a da aka ƙaƙaba wa mataimakin gwamna.
Ya kuma jero waɗanda yake tuhuma da suka ƙunshi gwamnatin Ondo, gwamna mai ci, majalisar dokoki da shugabanta, magatakardan majalisa da kuma Alkalin alƙalan Ondo, rahoton Leadership.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daibai Jami'ar Jihar Nasarawa
A wani ɓangaren kun ji cewa 'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare.
Hukumar makarantar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami'am tsaron jami'ar da hukumomin tsaro na kokarin ceto ɗaliban.
Asali: Legit.ng