Gaba Ta Kare: An Gano Wike a Gidan Saraki Bayan Rikicin Zaben PDP Na 2023
- Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya girgiza intanet bayan ya yi wani gagarumin yunkuri
- An gano tsohon gwamnan na jihar Ribas a gidan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a wani hoto da bidiyo da ya yadu
- Manyan yan siyasar biyu sun samu sabani tun gabannin zaben 2023 kuma alamu sun nuna sun dinke barakar da ke tsakaninsu
FCT, Abuja - Wani abun mamaki ya faru a daren ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, inda ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kai ziyarar bazata gidan tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar PDP ta rabu gida biyu, daya na tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sannan dayan na tare da Wike, wanda ya kasance gwamnan jihar Ribas a lokacin.
Barakar ta samo asali ne daga sabanin da aka samu wajen tsarin rabon mukamai na yanki-yanki, wanda yake a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsarin karba-karba na PDP
Tun 1999, PDP tana amfani da tsarin karba-karba wajen zabar yan takararta na kowani zangon zabe na shekaru hudu.
Sai dai kuma, abun ya sauya lokacin da PDP, a karo na farko karkashin jagorancin Sanata Iyorchia Ayu, ta ba kowani yanki damar shiga takarar kujeru, wanda ya kamata a bai wa yankin kudu.
A daya bangaren, Atiku ya fito daga yankin arewa kuma ya rigada ya yi amfani da tikitin arewa a zaben 2019.
Shawarar da Atiku ya yanke ya fusata manyan jiga-jigan PDP a kudu yankin da Wike ya fito. An dan samu saukin lamarin na dan lokaci, inda gaba daya yan takarar suka shiga zaben fidda gwani.
PDP ta rabu gida biyu
Sai dai kuma, a wannan lokacin jam'iyyar ta riga ta rabu gida biyu, da sansanin Atiku wanda ya kunshi Sanata Saraki, Aminu Tambuwal, Ahmad Fintiri da sauran jiga-jigan PDP daga arewa.
A bangaren Wike kuma, akwai jiga-jigan PDP daga kudu kamar su Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi.
Sai dai kuma, ziyarar da Wike ya kai gidan Saraki kwanan nan ya sauya tunanin cewa manyan jiga-jigan siyasar sun kawar da gabar da ke tsakaninsu.
Kotu ta tsige Sylva, dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a Bayelsa
A wani labarin, mun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Timipre Sylva, daga yin takara a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban.
Babbar kotun tarayyar ta yanke hukuncin ne a daren ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng