Gwamnan Delta Oborevwori Ya Nada Dan Takarar YPP a Babban Mukami
- Gwamna Oborevwori na PDP ya naɗa ɗan takarar Jam'iyyar adawa a matsayin mai ba shi shawara ta musamman a jihar Delta
- Wannan na zuwa ne sama da wata ɗaya bayan gwamnan ya naɗa ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP a matsayi mai gwaɓi
- Sakataren gwamnatin jihar Delta, Kingsley Emu, ya ce sabon naɗin zai fara aiki ne nan take
Jihar Delta - Gwamnan jihar Dleta, Sheriff Oborevwori, ya sake naɗa ɗan takarar gwamnan da suka fafata a zaben da ya gabata, a wata babbae kujera a gwamnati.
Daily Trust ta tattaro cewa a wannan karon gwamna Oborevwori ya naɗa ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar YPP, Sunny Ofehe, a matsayin mai taimaka masa kan harkokin waje.
Sunny Ofehe na jam'iyyar YPP na ɗaya daga cikin yan takarar da suka fafata a zaɓen gwamnan jihar Delta ranar 18 ga watan Maris, 2023 kuma shi ne na biyu da gwamnan ya ba muƙami.
Gwamnan, a ranar 4 ga Satumba, 2023, ya nada Goodnews Agbi, dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sa ido da tantance ayyuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren gwamnatin jihar Delta, Kingsley Emu, shi ne ya sanar da naɗin da gwamnan ya yi wa ɗan takarar YPP a matsayin mai taimaka masa kan hulɗa da harkokin waje.
A cewar Sakataren, wannan sabon naɗi da gwamna Oborevwori na jam'iyyar PDP ya yi, zai fara aike ne nan take babu ɓata lokaci, kamar yadda The Sun ta tattaro.
Takaitaccen bayani kan ɗan takarar na YPP
Mista Ofehe dan gwagwarmaya ne da ya yi fice a Najeriya da kasar Holland, kuma kwararre a fannin kare muhalli a yankin Neja Delta mai dumbin arzikin mai.
A tarihin gwagwarmayarsa ya fi mai da hankali musamman kan haƙƙin marasa ƙarfi da ayyukan kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa a matakin Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya.
Gwamna Abba Gida-Gida Ya Sanar da Ranar Ɗaura Auren 'Yan Mata da Zawarawa 1,800 a Kano
A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi ranar da za a ɗaura auren mutane 1,800 wanda gwamnatinsa ta ɗauki nauyi a jihar Kano.
Abba Gida-Gida ya kai ziyara hedkwatar hukumar Hisbah domin duba inda aka kwana dangane da shirye-shiryen bikin.
Asali: Legit.ng