Atiku Abubakar: Abin Da Ya Sa Shugaba Tinubu Ya Yi Wuf Ya Nada Sababbin Mukamai

Atiku Abubakar: Abin Da Ya Sa Shugaba Tinubu Ya Yi Wuf Ya Nada Sababbin Mukamai

  • ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya soki nade-naden da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a makon nan
  • Fela Durotoye ya shiga cikin masu taimakawa shugaban Najeriya a wajen yada labarai da hulda da al’umma
  • Kafin nan an nada Umar Tanko Yakasai, Abiodun Essiet, Abdulhamid Yahaya da kuma Emmanuella Eduozor

Abuja - Atiku Abubakar mai shari’a da Bola Ahmed Tinubu a kotu a kan zaben 2023, ya sake yin kaca-kaca da mai girma shugaban kasa.

Abin da ya jawo fushin Atiku Abubakar wannan karo shi ne nadin mukaman da Bola Tinubu ya yi, Premium Times ta kawo wannan rahoto.

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya fitar da jawabi ya ce karin hadimai a fannin yada labarai ba za su ceci Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu Ya Jawowa Mahaifinsa Suka Saboda Yawo a Jirgin Shugaban Kasa

Atiku Abubakar
Alhaji Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso a masallaci Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya ce karya Tinubu ya shirya

Mista Phrank Shaibu ya fitar da jawabi na musamman a madadin Atiku Abubakar, ya na zargin shugaban kasar da kafa sashen furofaganda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Ajuri Ngelale ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya nada karin wadanda za su rika taimaka masa a bangaren yada labarai a gwamnati.

Wadanda aka ba aikin sun hada da: Fela Durotoye, Fredrick Nwabufo da kuma Linda Akhigbe, sai kuma Aliyu Audu da Francis Adah Abah.

Hadimai ba su ceci Tinubu ba

Atiku ya ce ko hadimai dubu shugaban kasa Tinubu zai nada, ba za su kubutar da shi daga badakalar da ya tsunduma tsamo-tsamo ba.

"A ranar 18 ga watan Satumba na yi gargadi gwamnatin Tinubu ta fusata saboda ana ta bankado karyarsu, za su kafa sashen furofaganda.
Yanzu sun kafa sashen yada labarai da wayar da kan jama’a. wannan ya jawo adadin masu bada shawara kan harkar labarai sun kai 20.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Yadda Shari’ar Tinubu v Atiku Za Ta Kare a Kotun Koli

Kusan mutum uku daga cikin wadanda aka nada su na rike da mukami iri daya.
Mun fahimci yadda idon Tinubu ya rufe saboda ya na cikin badakalar karyar takardu kuma FBI za ta tona asirin harkar kwayoyinsa a Amurka."

- Phrank Shaibu

Shaibu ya ce mukarraban shugaban kasa wajen yada labarai sun fi masu bada shawara a kan tattalin arziki yawa saboda furofaganda.

2023: Shari'ar Tinubu da Atiku

A badakalar takardu da ake zargin Bola Tinubu, ku na da rahoto cewa tsofaffin ‘Yan majalisa da-dama ba su goyon bayan Atiku Abubakar.

Sanata Basheer Lado ya ce su na sane da zargin da yake kewaye da Shugaban kasar, ya na mai fatan kotun koli za ta wanke Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng