Takardun Tinubu: Yadda Kotun Koli Za Ta Iya Bai Wa Peter Obi Nasara, Lauyan Najeriya Ya Yi Bayani

Takardun Tinubu: Yadda Kotun Koli Za Ta Iya Bai Wa Peter Obi Nasara, Lauyan Najeriya Ya Yi Bayani

  • Nasarar Bola Tinubu na ci gaba da zama abar kalubalanta ga jam'iyyun adawa a fadin Najeriya.
  • Peter Obi na jam'iyyar LP ya shirya daukaka kara game da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wanda ta tabbatar da nasarar Tinubu
  • Tsohon gwamnan Anambra ya daukaka kara zuwa kotun koli, yan rokon kotun tayi watsi da hukuncin kotun baya tare da bayyana shi a matsayin shugaban kasa

Filato, Jos - An yi hasashen yadda makomar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, Peter Obi, ka iya kasancewa.

Peter Obi ya Peter Obi ya shirya kalubantar nasarar Tinubu

Idan za a iya tunawa kotun sauraron kararrakin zabe a ranar Laraba, 6 ga Satumba, da tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu da ya bawa Bola Tinubu nasarar zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

CSU: Keyamo Ya Bayyana Abin Da Atiku Zai Yi Don Nuna Tinubu Ya Kirkiri Takardar Karatu Ta Bogi

Kotun ta koma kori kararrakin da aka shigar ana kalubalantar nasarar Tinubu.

Sai dai, Obi bai gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ba ya kuma garzaya kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar na Labour ya ce kotun tayi kuskure a hukuncin ya kuma shigar da kararraki 51 gaban kotun koli yana rokon ta rushe hukuncin kotun baya ta kuma soke nasarar Tinubu.

A daya bangaren, dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ranar Alhamis, 5 ga Oktoba yayi kira ga Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da hada hannu da shi don yakar Tinubu da kuma APC.

Yayi kiran ne bayan jami'ar Chicago State University a Amurka ta saki tarihin karatun Tinubu ranar 2 ga Oktoba, wanda Atiku Abubakar ke zargin Tinubu da yin takardun bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164