Kotun Koli: “Kai Ta Shafa, Babu Ruwan Kwankwaso Da Shari’arka”, NNPP Ga Atiku

Kotun Koli: “Kai Ta Shafa, Babu Ruwan Kwankwaso Da Shari’arka”, NNPP Ga Atiku

  • Jam’iyyar NNPP ta ki amsa da tayin Atiku Abubakar na hada kai don ci gaba da shari'ar kalubalantar nasarar shugaban kasa Bola Tinubu a kotun koli
  • Jam'iyyar Kwankwaso ta gargadi Atiku da PDP akan su yi ta kansu, su bar neman janyo ta cikin abin da bai shafe ta ba
  • A ranar Alhamis ne Atiku ya roki Kwankwaso da Peter Obi don hada kai kan shari'ar da yake yi da Tinubu

Jam'iyyar NNPP ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da ya daina sako sunan Sanata Rabiu Kwankwaso a cikin karar da ya shigar don kalubakantar zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kotun koli, Daily Trust ta rahoto.

A yayin jawabinsa a taron manema labarai da ya kira a ranar Alhamis a Abuja, Atiku ya yi kira ga Peter Obi na Labour Party da Sanata Kwankwaso na NNPP da su zo su hada kai da shi don fallasa asirin shugaban kasa Tinubu.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan Jiga-Jigan PDP Da Suka Halarci Taron Da Atiku Ya Kira a Abuja

NNPP ta ce babu ruwanta da shari'ar Atiku da Tinubu
Kotun Koli: “Kai Ta Shafa, Babu Ruwan Kwankwaso Da Shari’arka”, NNPP Ga Atiku Hoto: @atiku/@KwankwasoRM
Asali: Twitter

Zaben shugaban kasa: NNPP bata shari'a da kowa a kotu

Sai dai kuma, da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar NNPP na kasa, mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Prince Nwaeze Onu, ya bayyana cewa sabanin Atiku da PDP, NNPP bata shari'a da kowa a kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onu ya jaddada cewa jam'iyyarsu bata je kotu don kalubalantar nasarar shugaban kasa Tinubu ba, saboda haka ba za ta yi shisshigi a abun da bai shafe ta ba, rahoton Aminiya.

Ya yi gargadin cewa kada wanda ya sako jam'iyyar NNPP cikin abun da ya shafi sauran jam'iyyu, cewa jam'iyyar ta yanke shawarar kin tunkarar kotu saboda soyayyar da take yi wa Najeriya.

Peter Obi ya nesanta kansa da shari'ar Atiku

A baya mun ji cewa, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ki amincewa da hadaka da Atiku don tabbatar da gaskiyar takardun Tinubu.

Kara karanta wannan

Dambarwar Satifiket: Lauya Ya Yi Hasashen Makomar Atiku Da Tinubu A Kotun Koli, Ya Fadi Dalilai

Obi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis ta bakin kakakin jam'iyyar, Obiora Ifoh inda ya ce shi ma kokari ya ke ya kwato hakkinsa, Legit ta tattaro.

The Nation ta tattaro Obi na cewa ya na kokari ne shi ma don kwato mulkin da aka kwace masa cikin zalunci lokacin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng