Jerin Jiga-Jigan PDP Da Suka Halarci Taron Da Atiku Ya Gudanar a Abuja

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Suka Halarci Taron Da Atiku Ya Gudanar a Abuja

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, bayan ya samu takardun karatun Shugaban kasa Bola Tinubu a jami'ar jihar Chicago.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sha caccaka kan gudanar da taron manema labarai ba tare da wani gwamna daga jam'iyyarsa ya hallara ba.

Atiku ya kira taron manema labarai a ranar Alhamis
Jerin Jiga-Jigan PDP Da Suka Halarci Taron Da Atiku Ya Gudanar a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Atiku ya zargi Tinubu da kirkirar satifiket din jami'ar jihar Chicago

A taron manema labaran, dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi zargin cewa Shugaban kasa Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da takardun karatu na bogi.

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, satifiket din jami'ar jihar Chicago da shugaban kasar ke yawo da shi mallakin wata bakar Ba'amurkiya ce.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa Wajen Fallasa Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin jiga-jigan PDP da suka halarci taron manema labaran sune:

1. Uche Secondus

Secondus ya kasance tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma dan gani kashenin Atiku a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

An tsige shi gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP domin ba da damar samar da shugaban jam'iyya na kasa daga arewa da kuma dan takarar shugaban kasa daga kudu, sai dai kuma Atiku ne ya samu tikitin.

2. Iyorchia Ayu

Ayu ne ya gaji Secondus a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa sannan ya samar da Atiku, dan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Bayan zaben fidda dan takarar shugaban kasar, sai kawunan jam'iyyar ya rabu kan Ayu. Rashin murabus dinsa daga matsayin shugaban jam'iyyar na kasa ne ya yi sanadiyar kayen da suka sha a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Takardun Tinubu: Atiku Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Ke Yaki Da Bola, Ya Nemi Goyon Baya

3. Sanata Ben Obi

Obi ya taba tsayawa a matsayin abokin takarar Atiku kuma ya yi aiki a matsayin minista lokacin da dan takarar shugaban kasar na PDP yake matsayin mataimakin shugaban kasa.

Ya kuma kasance darakta janar na kungiyar kamfen din Atiku/Okowa a jihar Anambra yayin zaben shugaban kasa na 2023.

Kalli bidiyon taron a kasa:

Shahararren lauya ya yi hasashen yadda shari'ar Tinubu da Atiku za ta kaya

A wani labarin, mun ji cewa wani kwararren lauya mai suna Titilope Anifowoshe ya yi martani kan dambarwar da ake tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Atiku na jam'iyyar PDP na kalubalantar zaben Bola Tinubu kan tafka magudi da kuma mallakar takardun bogi, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng