Shahararren Lauya Ya Yi Hasashen Yadda Shari'ar Tinubu Da Atiku Za Ta Kaya

Shahararren Lauya Ya Yi Hasashen Yadda Shari'ar Tinubu Da Atiku Za Ta Kaya

  • Titilope Anifowoshe, shahararren lauya a Najeriya ya yi fashin baki kan makomar shari'ar Atiku da Bola Tinubu
  • Anifowoshe ya ce babu alamar Atiku zai yi nasara a wannan dambarwar da ake ganin yadda Jami'ar Chicago ta tabbatar da gaskiya
  • Atiku na kalubalantar zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu

FCT, Abuja - Wani kwararren lauya mai suna Titilope Anifowoshe ya yi martani kan dambarwar da ake tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Atiku na jam'iyyar PDP na kalubalantar zaben Bola Tinubu kan tafka magudi da kuma mallakar takardun bogi, Legit ta tattaro.

Babban lauya ya bayyana abin da zai faru a shari'ar Atiku da Tinubu
Shahararren Lauya Ya Yi Martani Kan Shari'ar Tinubu Da Atiku. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Me Atiku ke karar Tinubu a kai?

A watan Satumba, kotun kararrakin zabe ta yi fatali da Atiku Abubakar kan rashin gamsassun hujjoji.

Daga bisani Atiku ya daukaka kara zuwa kotun koli don kwato hakkinsa na zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Fatali Da Rokon Atiku Na Neman A Hada Kai, Ya Bayyana Dalilansa Na Kin Amincewa

Atiku yayin ganawa da manema labarai a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba ya nemi hadin kan sauran 'yan takara da su ka hada da Rabi'u Kwankwaso da kuma Peter Obi.

Sai dai Peter Obi ya yi martani inda ya ce kowa ya ji da kansa don shi ma neman hakkinsa ya fito yi.

Me yasa Tinubu zai kayar da Atiku a kotun koli?

Lauya Anifowoshe ya shaidawa Legit cewa zai yi wahala Atiku ya yi nasara kan Bola Tinubu musamman kan maganar takardu daga Jami'ar Chicago.

Ya ce Jami'ar ta riga ta tabbatar da sahihancin takardun Tinubu inda ta ce tabbas ya halarci makarantar.

Ya ce:

"Dangane da makomar Atiku.
"Atiku ya bukaci sanin wasu abubuwa masu muhimmanci ta bakin lauyoyinsa.
"Misalin Difloma na Tinubu a Jami'ar Chicago a shekarar 1979.
"A bangare na, ban yi tsammanin Atiku zai samu nasara a wannan shari'ar ba ganin yadda Jami'ar ta tabbatar da cewa Tinubu dalibi ne a makarantar."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa Wajen Fallasa Tinubu

Atiku ya nemi hadin kan Kwankwaso da Peter Obi

A wani labarin, Atiku Abubakar ya bukaci hadin kan sauran 'yan takara don tabbatar da gaskiyar takardun Bola Tinubu.

Atiku na magana ne kan Rabiu Kwankwaso da kuma Peter Obi don su hada karfi da karfe don kwato hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.