Peter Obi Ya Ki Amincewa Da Rokon Atiku Na Hada Kai A Kotun Zabe
- Peter Obi ya ki amincewa da tayin Atiku Abubakar na hada kai don ci gaba da shari'ar tabbatar da gaskiya kan takardun Tinubu
- Atiku a jiya Alhamis ya roki 'yan takarar jam'iyyun NNPP da Labour, Kwankwaso da Peter Obi don hada kai kan shari'ar da su ke
- Peter Obi a martaninshi, ya yi fatali da rokon na Atiku inda ya ce shi ma nema wa kansa hakki ya ke da aka kwace masa
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ki amincewa da hadaka da Atiku don tabbatar da gaskiyar takardun Tinubu.
Obi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis ta bakin kakakin jam'iyyar, Obiora Ifoh inda ya ce shi ma kokari ya ke ya kwato hakkinsa, Legit ta tattaro.
Wane kira Atiku ya yi wa Peter Obi da Kwankwaso?
A jiya ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi goyon bayan sauran 'yan takara don ci gaba da kalubalantar takardun Tinubu a kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar jam'iyyar ta ce:
"Obi na kokarin ganin ya nemo 'yanci ga kasa inda adalci zai yi aiki don tabbatar da shugabanci mai nagarta.
"Obi a lokuta da dama na kokarin ganin an samu shugabannin da jama'a za su na kwaikwayo."
Meye Peter Obi ya ce kan rokon Atiku?
"Hakan ne ma ya sa ya bayyana takardunsa don tantancewa inda ya ce Najeriya za ta samu ci gaba ne idan shugabanninta su ka zama ma su gaskiya."
The Nation ta tattaro Obi na cewa ya na kokari ne shi ma don kwato mulkin da aka kwace masa cikin zalunci lokacin zabe.
A karshe ya yi kira ga duk masu neman adalci ya dore a kasar da su zo don hada kai da cimma abin da ake nema.
Atiku ya roki Kwankwaso, Peter Obi hadin kai kan Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya roki 'yan jam'iyyun adawa da su zo su hada kai don kwato wa talakawa 'yancinsu.
Atiku na magana musamman kan Rabiu Kwankwaso da kuma Peter Obi yayin da su ke kalubalantar zaben shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng