Atiku Ya Bayyana Cewa Ya Na Yaki Ne Da Tinubu Don Kwato Wa 'Yan Najeriya Hakkinsu
- Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce ya na yaki kan wannan shari'a ce don 'yan Najeriya
- Atiku ya ce ya na gwagwarmaya ne don tabbatar da cewa an samu shugabanci mai inganci a kasar
- Ya roki Kwankwaso da Peter Obi da su hada kai don tabbatar da gaskiya kan takardun Tinubu
FCT, Abuja - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa wannan gwagwarmaya da ya ke yi don 'yan Najeriya ne.
Atiku ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja a yau Alhamis 5 ga watan Oktoba.
Meye Atiku ya ce kan shari'a da Tinubu?
Ya ce yakin da ya ke yi don tabbatar da gaskiyar takardun Tinubu ya na yi ne don inganta rayuwar al'ummar Najeriya, Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce hakan shi zai ba da damar tabbatar da gaskiya ga ma su mulki da kuma wakilci nagari.
Taron wanda ya samu rakiyar gwamnonin PDP da kuma jiga-jigan jam'iyyar sun yi alkawarin kai shari'ar har kwano don tabbatar da gaskiya.
Wane sako Atiku ya tura ga 'yan Najeriya kan Tinubu?
A yayin jawabinshi, Atiku ya roki Peter Obi da Rabi'u Kwankwaso da su zo a hada kai don tabbatar da gwamnati mai inganci a kasar.
'Yan jam'iyyun adawa da su ka hada da PDP da NNPP da kuma Labour na kalubalantar sahihancin zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.
A cikin watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zabe ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin halastaccen zababben shugaban kasa, Daily Post ta tattaro.
Lauyan Atiku Ya Bayyana Abubuwan Da Suka Bankado Dangane Da Takardun Karatun Da Tinubu Ya Gabatarwa INEC
Bayan yanke hukuncin, Atiku da Obi na jam'iyyun PDP da Labour sun daukaka kara don kwato abin da su ke ganin zalunce ne.
'Ban yarda da tikitin Musulmi da Musulmi ba', Atiku
A wani labarin, Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce tikitin Musulmi da Musulmi bai dace da Najeriya ba.
Atiku ya ce ko shi ne a matsayin Tinubu ba zai yadda da wannan tsari na rashin adalci ba.
Asali: Legit.ng