Atiku Ya Ce Tikitin Musulmi Da Musulmi Bai Dace Da Najeriya Ba Kwata-kwata

Atiku Ya Ce Tikitin Musulmi Da Musulmi Bai Dace Da Najeriya Ba Kwata-kwata

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce a tsarin Najeriya bai kamata a yi tikitin Musulmi da Musulmi ba
  • Atiku ya ce kwata-kwata tsarin bai karbi Najeriya ba da ke da addinai da al'adu daban-daban a kasar wanda dole a yi duba gare su
  • Dan takarar PDP ya bayyana haka ne a yau Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Abuja

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce kwata-kwata tsarin tikitin Musulmi da Musulmi bai dace da Najeriya ba.

Atiku ya bayyana haka a yau Alhamis 5 ga watan Oktoba a Abuja yayin hira da manema labarai.

Ban yadda da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi ba, Atiku ya magantu
Atiku Ya Soki Tikitin Musulmi Da Musulmi. Hoto: Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Meye Atiku ya ce kan tikitin Musulmi da Musulmi?

Ya soki tsarin tikitin Musulmi da Musulmi inda ya ce bai dace da kasa irin Najeriya ba da ke sa addinai daban-daban, Channels TV ta tattaro.

Kara karanta wannan

Takardun Tinubu: Atiku Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Ke Yaki Da Bola, Ya Nemi Goyon Baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Har yau, ba zan yi tikitin Musulmi da Musulmi ba, ko da ba zan zama shugaban kasa ba saboda ban yarda da tsarin ba.
"Bai dace ba, kwata-kwata bai dace da kasa irin Najeriya mai addinai da al'adu daban-daban ba, bai kamata gwamnati ta manta da wannan bambanci ba."

Atiku ya kuma roki 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour da NNPP, Peter Obi da Rabi'u Kwankwaso da su zo su taya shi don tabbatar da gaskiya a takardun Tinubu.

Meye jama'a su ka cewa Legit Hausa kan bayanin Atiku?

Kwamred Mustapha ya ce:

"In shaa Allah Atiku da mulki har abada kuma mun gane inda ya dosa Musulunci ya ke yaka."

Bashir Sulaiman ya ce da yardar Allah sai dai ya ga ana mulki a Najeriya.

Aliyu Abubakar ya ce:

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

"Daman yaudarar mu aka yi da tsarin, mu na fada wa mutane a lokacin su na ganin kamar ba ma kishin addini ne."

Atiku ya fadi dalilin shari'a da Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce ya na yaki ne don 'yan Najeriya.

Atiku ya bayyana cewa ya na nema wa 'yan Najeriya ne shugabanci mai inganci da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.