Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

  • Alhaji Atiku Abubakar, ya mika muhimmin kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na jam'iyyar Labour
  • Dan takarar shugaban kasar na PDP ya roki takwarorinsa su hada kai da shi domin ganin an kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki
  • Atiku ya yi wannan kiran ne yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Alhamis bayan kotu ta bashi izinin samun takardun karatun Tinubu daga CSU

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya yi kira ga takwarorinsa na jam'iyyar Labour da NNPP, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su hada kai da shi a kokarinsa na korar Tinubu daga kujerar shugaban kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne yayin jawabinsa na kai tsaye da wakilin Legit Hausa ya bibiya a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, game da abubuwan da suka bayyana a baya-bayan nan kan takardun Tinubu a Jami'ar Jihar Chicago, CSU.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Ya Bayyana Dan Najeriya Da Ya Karfafa Masa Gwiwa Ya Binciki Tarkardun Tinubu

Atiku ya nemi hadin kan Peter Obi da Kwankwaso
Atiku ya bukaci Kwankwaso da Peter su mara masa baya don korar Tinubu. Hoto: Photo Credit: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Kwankwaso
Asali: Twitter

Atiku ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da shugabannin addini su hada kai da shi bisa aikin da ya sa gaba dangane da takardun karatun Shugaba Tinubu a Jami'ar Chicago.

Ya kuma jadada yardarsa da dimokradiyya, ya kara da cewa yana yi wa Najeriya, kasar da ya ke kauna sosai yaki ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Atiku:

"Mutane na sa mana ido domin su ga mun bi doka tare da kare su."

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu izini daga kotu wacce ta tilasta Jami'ar Chicago ta mika masa takardun Tinubu.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164