Tsohuwar Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Binta Bello, Ta Fice Daga PDP

Tsohuwar Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Binta Bello, Ta Fice Daga PDP

  • Fatima Binta Bello, 'yar majalisar da ta wakilci mazabar Kaltungo/Shongom a majalisar wakilan tarayya ta 8 ta fice daga PDP
  • Tsohuwar mai tsawatarwa ta marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ta fito ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba
  • Sai dai Binta Bello ba ta ce komai ba game da dalilin da ya sa ta yanke barin jam'iyyar PDP da kuma jam'iyyar da zata koma ba

FCT Abuja - Tsohuwar mataimakiyar mai tsawatarwa ta marasa rinjaye a majlisar wakilan tarayya, Fatima Binta Bello, ta fice daga jam'iyyar PDP.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Binta Bello, ta miƙa wasiƙar fice wa daga PDP ga shugaban jam'iyyar na gundumar Shongom, ƙaramar hukumar Shongom a jihar Gombe ranar Alhamis.

Tsohuwar 'yar majalisa daga jihar Gombe, Fatima Binta Bello.
Tsohuwar Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Binta Bello, Ta Fice Daga PDP Hoto: @Honbintab
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa ɗaukar matakin barin PDP na da wahala matuƙa, amma bisa tilas ta yanke shawarin hakan bayan tattauna wa da na kusa da ita a fagen siyasa.

Kara karanta wannan

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazanar Kashe Mataimakin Tinubu, Gawuna da Alƙalai a Bidiyo

Sai dai tsohuwar mamban majalisar tarayyan ba ta bayyana ainihin abinda ya jawo ta bar babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar nan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasiƙar da ta rubuta, Binta Bello ta ce:

"Na rubuto wannan takardar ne domin sanar da murabus ɗina daga matsayin mambar jam'iyyar PDP nan take. Haɗe da wannan takarda ga katin mambana na PDP nan."

Wace jam'iyya zata koma bayan fita daga PDP?

Haka nan kuma tsohuwar 'yar majalisar ba ta fayyace cewa ga jam'iyyar siyasar da ta zaɓi koma wa ba bayan barin PDP, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Ta shafe shekaru takwas a majalisar wakilan tarayya tana wakiltar mazaɓar Kaltungo da Shongom daga jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas.

Bugu da ƙari, Binta Bello ta kasance tsohuwar mataimakiyar shugaban ƙaramar hukumar Shongom, sannan ta riƙe kujerar kwamishina a zamanin mulkin Ɗanjuma Goje.

Kara karanta wannan

To fah: Inuwar lema ta dauki dumi, tsohon gwamnan Kaduna ya fice daga PDP

Kotu Ta Tabbatar Da Nasir Idris a Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi

A wani rahoton kuma Kotun zaɓe ta yanke hukunci kan ƙarar da ta kalubalanci nasarar gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi a zaɓen watan Maris, 2023.

Yayin zaman yanke hukunci ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, 2023, Kotun ta tabbatar da nasarar gwamna Nasir da mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262