Atiku Zai Shigar Da Kara a Gaban Kotun Koli Bayan Samun Takardun Bayanan Karatun Tinubu

Atiku Zai Shigar Da Kara a Gaban Kotun Koli Bayan Samun Takardun Bayanan Karatun Tinubu

  • Jami'ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka, ta fitar da bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu ga babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar
  • Jami’ar ta miƙa takardun ga lauyoyin Atiku biyo bayan zaman kotu da muhawara tsakanin lauyoyin Atiku da Tinubu
  • Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya garzaya wata kotu a Amurka domin ta tilasta wa jami'ar sakin bayanan karatun Tinubu

Chicago, Amurka - Bayan samun takardun bayanan karatun Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa umarnin wata kotun Illinois da ke Chicago, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai shigar da ƙararsa a kotun ƙoli a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

Atiku, wanda ya fafata da Tinubu a zaɓen watan Fabrairun 2023, ana sa ran zai shigar da takardun da ya samu daga jami'ar jihar Chicago (CSU) domin cigaba da ɗaukaka ƙarar da yake kan zaɓe a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Canza da Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Tinubu

Atiku zai shigar da kara a kotun koli
Atiku ya dade yana neman samun takardun bayanan karatun Tinubu Hota: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku zai kai Tinubu ƙara a kotun ƙoli

Idan ba a manta ba jami'ar ta fitar da bayanan karatun shugaban ƙasar a farkon makon nan kuma magatakardar CSU, Caleb Westberg, shi ma ya gabatar da takardun a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, bisa bin umarni ga hukuncin da alƙalin kotun Jeffrey Gilbert ya yanke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 19 ga watan Satumba ne Gilbert ya amince da buƙatar Atiku na sakin takardun bayanan karatun Tinubu amma shugaban ƙasar ya shigar da ƙorafin a sake duba umarnin.

Wasu majiyoyi na kusa da Atiku sun tabbatar wa jaridar The Punch a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba cewa Atiku a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba zai gabatar da sabbin shaidu kan Tinubu a gaban kotun ƙoli.

Jaridar ta ruwaito majiyar na cewa:

"Me yasa Atiku ba zai gabatar da sabbin shaidun da aka samu daga CSU ba gobe (yau)? Atiku bai je Amurka domin samun bayanan ko shaidun da zai ba wa mai siyar da ƙosai ba. Zai gabatar da sabbin shaidu gobe (Alhamis, 5 ga Oktoba)."

Kara karanta wannan

Takardun Karatun Tinubu: Jam'iyyar APC Ta Yi Wa Atiku Da PDP Shagube, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Atiku Zai Yi Jawabi Kan Takardun Tinubu

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, zai yi magana kan takardun bayanan karatun Shugaba Tinubu.

An daɗe ana taƙaddama kan takardun karatun Tinubu bayan Atiku ya shigar da ƙara a kotu yana neman ta tilasta jami'ar CSU ɗamka masa takardun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng