Minista Balarabe Ya Bayyana Dalilin Sumansa A Majalisa Yayin Tantance Shi A Yau
- Minista Balarabe Abbas ya bayyana dalilin faduwarshi a majalisar Dattawa yayin da ake tantance shi a yau Laraba
- Balarabe wanda shi ne ya maye gurbin El-Rufai daga jihar Kaduna ya suma ana tsaka da tantance shi a yau
- Ya bayyana wa shugaban majalisar, Goswill Akpabio cewa ya shafe kwanaki uku ya na aiki ba tare da hutawa ba
FCT, Abuja – Sabon minista daga jihar Kaduna ya bayyana dalilin sumansa a majalisar Dattawa a yau yayin tantance shi a dakin majalisar.
Balarabe Lawal ya fadi kasa lokacin da ake tantance shi a yau Laraba 4 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.

Source: UGC
Meye ya jawo faduwar ministan a majalisar?
Faduwarshi ke da wuya, shagaban majalisar ya bukaci a kawo masa dauki inda ya farfaɗo bayan wani lokaci.

Kara karanta wannan
Yanzu Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Zababben Ministan Da Ya Yanke Jiki Ya Fadi Da Wasu 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Balarabe daga bisani ya shaidawa shugaban majalisar, Godswill Akpabio dalilin faduwar tashi lokacin da ake tantance shi.
Balarabe ya bayyana cewa gajiya ce da ya yi ta jawo masa wannan matsalar inda ya ce ya shafe kwanaki da dama ya na aiki ba tare da hutawa ba, Aminiya ta tattaro.
A jita Talata ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika karin sunayen ministoci majalisar Dattawa don tantancewa.
Bayan Balarabe ya gabatar da kanshi da tarihin rayuwarshi kawai sai ya fadi kasa wanda tuni aka kawo masa agajin gaggawa.
Wane mataki majalisar ta dauka bayan suman ministan?
Shugaban majalisar, ya bukaci masu daukar hoto da faifan bidiyo da su dakata da dauka.
Majalisar ta shiga wani zama na sirri yayin da ake kula da lafiyar ministan a bayan fage inda aka dauke shi a motar daukar marasa lafiya zuwa asibiti.
Balarabe shi ne wanda ya maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai a matsayin wakilin daga jihar Kaduna a Arewacin kasar.

Kara karanta wannan
Da Dumi-Dumi: An Bayyana Halin Da Wakilin Jihar Kaduna Yake Ciki Bayan Ya Kife a Wajen Tantance Ministoci
El-Rufai ya rasa wannan damar ce bayan majalisar ta ki tabbatar da shi saboda matsalar da ta shafi tsaro.
Sabon minista ya suma a gaban majalisa yayin tantancewa
A wani labarin, sabon minista daga jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya suma a gaban majalisa yayin da ake tantance shi.
Balarabe shi ya maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai bayan rasa wannan damar.
Asali: Legit.ng