Abinda Ya Sa Na Jagoranci Mambobin NWC Zuwa Wurin Buhari, Ganduje Ya Magantu
- Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya jagoranci tawagar mambobin NWC zuwa wurin Buhari ne domin ya gabatar da su
- Shugaban APC na ƙasa ya ce sun kuma taya tsohon shugaban ƙasar murnar ranar samun 'yancin kan Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kano ya kuma nuna farin cikinsa bisa nasarorin da APC ta samu a Kotunan zaɓe zuwa yanzu
FCT Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi ƙarin haske kan ziyarar da tawagar kwamitin gudanarwa na APC (NWC) suka kai wa Muhammadu Buhari.
Ganduje ya bayyana cewa ya jagoranci tawagar mambobin NWC zuwa wurin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ne domin ya gabatar masa da su matsayinsa na jagora.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar Ganduje ta ziyarci tsohon shugaban kasar a mahaifarsa da ke Daura a jihar Katsina ranar Litinin.
Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya tabbatar da haka a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na Kano ya ce tawagar ta kuma taya Buhari murnar cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Muhimmin abinda ya kai mu wurin Buhari - Ganduje
“Babban maƙasudi shi ne mu gabatar da sabon kwamitin NWC na jam'iyyar mu ta ƙasa. Sannan kuma mu nuna masa ana tare da kuma gode masa bisa hidimar da ya yi wa kasar nan cikin shekaru takwas.”
“Kuma mu taya shi murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai, shekaru 63 na ci gaban Nijeriya wanda daga ciki harda shekaru 8 na gwamnatinsa. Shi ya sa muka je gidansa na Daura, kuma mun gode masa da ya karbe mu.”
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Dangane da nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a kotunan zaɓe kawo yanzu, Ganduje ya ce:
"Hakika, gani ya kori ji, mun ji dadi sosai mun gamsu, amma hakan bai wadatar ba. Muna da zabukan da za a yi a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo. In sha Allahu mu za mu samu nasara."
Gwamna Abdullahi Sule Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe
A wani rahoton kuma Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce zai daukaka hukuncin da Kotun zabe ta yanke zuwa gaba domin kwato hakkinsa.
A ranar Litinin, Kotun zabe ta tsige Sule kuma ta ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya ci zaben watan Maris.
Asali: Legit.ng