Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara Na Jihar Ribas

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara Na Jihar Ribas

  • Kotun zabe ta sanar da hukuncin da ta yanke kan karar da ɗan takarar LP ya kalubalanci nasarar gwamna Fubara na jihar Ribas
  • A zaman yanke hukunci ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, Kotun ta kori ƙarar bisa rashin cancanta da gaza tabbatar da zargi
  • Gwamna Fubara na jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ribas a ranar 18 ga watan Maris, 2023

Abuja - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Ribas mai zama a birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar Labour Party ya shigar gabanta.

Daily Trust ta tattaro cewa Kotun ta ƙori ƙarar wacce Beatrice Itubo, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar LP ya shigar inda ya ƙalubalanci nasarar PDP.

Gwamnan jihar Ribas, Simnalayi Fubara.
Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara Na Jihar Ribas Hoto: Simnalayi Fubara
Asali: Facebook

Wannan ƙara dai ta ƙalubalanci nasarar Gwamna Simnalayi Fubara na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Babban Gwamnan APC a Jihar Arewa

Fubara ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Ribas ne da ƙuri'u 302,614, ya lallasa babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Tonye Cole, wanda ya samu ƙuri'a 95,274.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa rashin gamsuwa da sakamakon zaben, wanda hukumar INEC ta bayyana, 'yan takarar jam'iyyun APC da LP suka garzaya suka shigar da ƙara gaban Kotun zaɓe.

Kotu ta yi watsi da ƙarar Labour Party

Bayan karban rubutaccen bayanan rufewa daga kowane ɓangare, kwamitin alƙalan Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Cletus Emifonye ya yanke hukunci ranar Litinin 2 ga watan Satumba, 2023.

Kotun ta ƙori ƙarar jam'iyyar LP bisa hujjar rashin cancanta da kuma gazawar ɓangaren masu ƙara wajen tabbatar da zarge-zargen da su ke a gaban Kotu.

Channels TV ta tattaro cewa a ranar 13 ga watan Satumba, 2023, Kotun zaɓen ta tanadi hukuncinta kan ƙararrakin da suka ƙalubalanci nasarar PDP a zaben gwamnan jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamna Sule Na Nasarawa, Ta Tabbatar Da PDP

A wani rahoton na daban kotun sauraran kararrakin zabe ta kori Gwamna Sule Abdullahi na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta kuma tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262