Gwamnan Jihar Sokoto Ya Yaba Da Hukuncin Kotu Bisa Tabbatar Da Nasararsa

Gwamnan Jihar Sokoto Ya Yaba Da Hukuncin Kotu Bisa Tabbatar Da Nasararsa

  • Gwamnan jihar Sokoto ya nuna farin cikinsa bayan kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar
  • Dr. Ahmed Aliyu ya yaba da hukuncin kotun inda ya ce ta yi adalci wajen korar ƙarar da jam'iyyar PDP ta gabatar
  • Gwamnan ya kuma shawarci ƴan adawa da su zo su haɗa hannu da gwamnatinsa domin ciyar da jihar gaba

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, ya yaba da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar da ke zamanta a Sokoto ta yanke, inda ta tabbatar da nasararsa a zaɓen da aka gudanar a jihar, cewar rahoton Punch.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Abubakar Bawa ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa fatali da ƙarar da jam’iyyar PDP ta gabatar wa kotun, ya nuna ƙarara cewa ba su da gaskiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP

Gwamna Ahmed Aliyu ya yaba da hukuncin kotu
Gwamnan Sokoto ya yaba da hukuncin kotun zabe Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Wani ɓangare na sanarwar:

"Hukuncin da kotun ta yanke, shaida ce ƙarara na yadda bangaren shari'ar ƙasar nan ya kasance mara son rai, hukunci abun farin ciki ne ga al'ummar jihar da kuma duk masu son tabbatar da dimokuraɗiyya a ciki da wajen Najeriya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yabawa kotun kan cewa ta yi abin da ya dace da kuma yin adalci bayan jin ta bakin duk masu ruwa da tsaki a cikin karar waɗanda ke ƙalubalantar sahihancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen 2023, rahoton Tribune ya tabbatar.

Gwamnan ya yi kira ga ƴan adawa a jihar da su hada kai da gwamnatinsa domin ciyar da jihar gaba, yana mai cewa kishin jihar ne abin da ya kamata a yanzu a zama abin da zai zama sanadin bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙin jihar.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Ya kuma kara tunatar da ƴan adawar cewa 2027 ba ta yi nisa ba domin haka akwai bukatar su jajirce domin fafutukar yaƙi na gaba domin zaben 2023 an yi shi an wuce wajen.

Dan Takara Ya Kasa Biyan Bashi

A wani labarin kuma, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Delta ya koka kan basussukan da suka yi masa katutu.

Harrison Gwamnishu wanda ya yi takarar ɗan majalisar dokokin jihar, kuma bai yi nasara ba, ya ce basussukan da ke kansa sun sanya shiga yanayi na rashin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng