Delta: Dan Takarar LP a Zaben 2023 Ya Koka Kan Bashin Da Ya Yi Masa Katutu

Delta: Dan Takarar LP a Zaben 2023 Ya Koka Kan Bashin Da Ya Yi Masa Katutu

  • Ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jihar Delta ya sanya kansa cikin rigimar bashi saboda zaɓen 2023
  • Harrison Gwamnishu wanda ya yi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party, ya koka cewa ya kasa biyan bashin da ake binsa
  • Gwamnishu ya yi nuni da cewa rashin iya biyan bashin ya sanya ya shiga cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali

Jihar Delta - Ɗaya daga cikin ƴan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Harrison Gwamnishu, ya ce ana binsa ɗumbin bashi wanda ya hana shi samun kwanciyar hankali.

Gwamnishu wanda dan rajin kare haƙƙin ɗan Adam ne ya tsaya takarar ɗan majalisar dokoki a jihar Delta a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, amma bai yi nasara ba.

Dan takarar LP ya kasa biyan bashi
Harrison Gwamnishu ya kasa biyan bashin da ya ci lokacin zabe Hoto: Harrison Gwamnishu
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, ya bayyana yadda yake ta faman biyan basussukan da ya ci kafin zaɓen da yadda kasuwancinsa ya samu tawaya.

Kara karanta wannan

Abdullahi Adamu Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu 1 Da Tinubu Ya Gaya Masa Bayan Ya Yi Murabus Daga Shugabancin APC

Harrison ya kasa biyan bashin da ya ci

Ya ce ya sayar da wasu kadarorinsa ciki har da mota a kokarinsa na biyan bashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnishu ya ce zai sauka daga mukaminsa na shugaban tawagar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da ke ƙarƙashinsa har sai ya warware matsalar.

"Ina sanar da ku cewa ina cikin tsananin BASHI kuma ba ni da kwanciyar hankali hakan ya sanya na yi wannan rubutun. Wasu abokai sun tuntuɓe ni inda suka bani shawarar na fito na bayyana halin da na ke ciki."
"Ban zalunci kowa ba. Kasuwanci na ya samu tawaya wanda za a iya tabbatar da hakan. Wasu abokaina sun ba ni lamuni a lokacin zaɓe."
"Na yi kokarin biya ta hanyar sayar da motata da aka ba ni kyauta kuma na sayar da wasu kadarori na don biyan wannan bashin. Na sanya musu lokaci kuma na kasa saboda ba ni da wata hanyar da za ta iya biyan wannan bashin."

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Bayan Rufin Wani Gini Ya Rufto a Jihar Taraba

"Barci ya gagare ni, na rasa abokai kuma ban taɓa tunanin zan taɓa shiga cikin wannan yanayin ba. Mahaifina yanzu haka yana fama da ciwo saboda wannan abun domin wasu daga ciki sun je har gida sun yi wa iyayena barazana."
"Ƙaunar da nake yi wa jama'a ba ta hana ni samun matsaloli a rayuwata ba. Don Allah waɗanda suke koyi da ni suka ji na ba su kunya, ku yi hakuri da wannan halin da nake ciki. Ni mutum ne kuma ni ma zan iya yin kuskure, amma ba shakka ba ni ba ɗan zamba ba ne."

Adamu Ya Yi Magana Kan Nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya yi magana kan nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen 2023.

Tsohon shugaban wanda ya yi murabus jim kaɗan bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa, ya bayyana cewa ya ji daɗi cewa shi ne ya gaji tsohon Shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng