Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Agbu Kefas a Matsayin Gwamnan Jihar Taraba
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Taraba ta tabbatar da nasarar da gwamna Agbu Kefas ya samu a zaɓen gwamnan jihar
- Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar NNPP ta shigar tana ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu
- Hukuncin da kotun ta yanke ya yi wa magoya bayan jam'iyyar PDP daɗi, waɗanda suka fito kan titunan birnin Jalingo suna murna
Jihar Taraba - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Taraba, ta tabbatar da Agbu Kefas na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Taraba.
Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa kotun mai alƙalai uku ta bayyana cewa ƙarar jam'iyyar NNPP da ɗan takararta Yahaya Sani, da ke ƙalubantar zaɓen Kefas a matsayin gwamnan jihar, ba ta cancanta ba wanda hakan ya sanya ta yi fatali da ita.
Jam’iyyar NNPP da dan takararta sun shigar da ƙara ne a kan nasarar da PDP da ɗan takararta gwamna Kefas suka samu a zaben gwamna, bisa zargin cewa an tafka maguɗi da rashin bin dokar zaɓe, yaga takardun sakamakon zaɓe da tayar da rikici a lokacin zaɓen.
Kotun ta yanke hukuncin cewa mai shigar da ƙara da ke ikirarin ya samu rinjayen ƙuri'un da aka kaɗa ya ruɗe domin yana neman a bayyana zaɓen wanda sahihi ba, kuma yana son a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene ra'ayin lauyoyi kan hukuncin?
Lauyoyin gwamnan da na hukumar zaɓe ta INEC, sun ce hukuncin abin farin ciki ne kuma ba su ga dalilin ɗaukaka ƙara ba, cewar rahoton The Punch.
Mataimakin gwamnan jihar Aminu Alkali wanda ya kasance a kotun ya nemi abokan adawarsu da suka shigar da ƙarar da su gabatar da shirye-shiryensu na cigaban jihar ta yadda za a haɗa kai a ciyar da jihar gaba.
A zaɓen da ya gabata, jam'iyyar PDP da ɗan takararta sun yi nasara a ƙananan hukumomi 11, NNPP ta yi nasara a ƙananan hukumomi uku, yayin da APC ta lashe ƙananan hukumomi biyu kacal.
Magoya bayan jam'iyyar PDP sun fito kan titunan birnin Jalingo suna murnar nasarar da gwamnan ya samu a kotun.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Aliyu
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta tabbatar da nasarar gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Saidu Umar suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng