Ministan Tinubu, Mataimakin Gwamna da Sanata Sun Dira Kotun Zaben Jihar Ogun

Ministan Tinubu, Mataimakin Gwamna da Sanata Sun Dira Kotun Zaben Jihar Ogun

  • Manyan jiga-jigan gwamnatin APC ciki harda Ministan Bola Tinubu sun halarci zaman yanke hukunci a Kotun zaben gwamnan Ogun
  • Mataimakin gwamna, Sanata da ɗan majalisar wakilan tarayya duk sun hallara yayin da alkalai zasu yanke makomar gwamna Abiodun na APC
  • Tun da safe jami'an tsaro suka mamaye harabar Kotun tare da toshe hanyoyin zuwa domin hana zirga-zirga

Jihar Ogun - Ƙaramin ministan muhalli, Dakta Iziaq Kunle Salako da mataimakin gwamnan jihar Ogun, Noimot Salako-Oyedele, sun isa Kotun sauraron ƙarar zaben gwamna mai zama a Abeokuta.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Sanata mai wakiltar mazaɓar Ogun ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Olamilekan Adeola, da sauran ƙusoshin gwamnati sun halarci zaman Kotun.

Kotun zaben jihar Osun.
Ministan Tinubu, Mataimakin Gwamna da Sanata Sun Dira Kotun Zaben Jihar Ogun Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sanata Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, ya dira harabar Kotun da misalin ƙarfe 7:55 na safiyar ranar Asabar, yayin da Ministan ya ƙariso mintuna kaɗan bayan haka.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Gwamnan APC Ke Shirin Tantance Makomarsa a Kotun Zaɓe

Sun halarci zaman yanke hukuncin tare da rakiyar manyan muƙarraban gwamna Dapo Abiodun, daga ciki har da kwamishinoni da mataimakin shugaban ma'aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, mamban majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tunji Akinosi, shi ma ya isa Kotun a halin da ake ciki, rahoton Headtopics ya tattaro.

Kwamitin Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Hamidu Kunaza, zai yanke hukunci kan ƙarar da aka ƙalubalanci nasarar Gwamna Abiodun na APC a zaɓen 18 ga watan Maris.

Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta na gwamna a zaben da ya gabata, Ladi Adebutu, ne suka shigar da ƙarar suna masu ƙalubalantar sakamakon da INEC ta sanar.

An girke tulin jami'an tsaro

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun da misalin ƙarfe 6:00 na safiya jami'an tsaro suka mamaye harabar Kotun don komai ya tafi cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

An toshe baki ɗaya titunan da ke zuwa Kotun domin hana zirga-zirgar jama'a da ababen hawa yayin da jami'an tsaro suka girke motocin sulƙe biyu a kofar shiga.

Shin Da Gaske An Sanya Wa Ministar Tinubu Guba? Gaskiya Ta Bayyana

A wani rahoton na daban Ma'aikatar kula da wuraren tarihi da buɗe ido ta musanta rahoton da ke yawo a soshiyal midiya cewa minista, Lola Ade-John, ta ci guba.

Raɗe-raɗi ya yaɗu a kafafen sada zumunta cewa ministar na kwance a Asibitin Abuja bisa zargin an ba ta guba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262