Tashin Hankali Yayin da Gwamnan Delta Zai San Makomarsa Gobe Jumu'a
- An shiga yanayin tashin hankali yayin da Kotun zaɓe ta ce zata yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Delta gobe Jumu'a
- Manyan jam'iyyun adawa APC, LP da SDP ne suka shigar da ƙara suna masu ƙalubalantar nasarar gwamna Oborevwori na PDP
- INEC ta ayyana ɗan takarar PDP mai mulki a jihar Delta, Oborevwori a matsayin wanda ya ci zaɓen 18 ga watan Maris, 2023
Jihar Delta - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Delta ta shirya yanke hukunci kan nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori na jam'iyyar PDP.
Kwamitin alƙalan Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a C.H Ahuchaogu zai yanke hukunci kan ƙarar idan Allah ya kaimu gobe Jumu'a, 29 ga watan Satumba, 2023.
Yadda shari'ar ta gudana
The Nation ta tattaro cewa jam'iyyar Labour Party, Social Democratic Party (SDP), da jam'iyyar APC ne suka shigar da ƙara gaban Kotu suna kalubalantar nasarar gwamna Oborevwori.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana ɗan takarar PDP, Oborevwori, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Delta a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Bisa rashin gamsuwa da sakamakon da INEC ta sanar, jam'iyyun uku suka garzaya Kotun zaɓe, inda suka roƙi a soke nasarar jam'iyyar PDP.
Manyan abokan hamayyar gwamna Oborevwori da zaɓen da ya gabata sun haɗa da ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Sanata Ovie Omo-Agege, da na SDP, Chief Kenneth Gbagi, da Ken Pela na LP.
Dukkan ɓangarorin da ƙarar ta shafa sun gabatar da rubutaccen bayaninsu na ƙarshe a watan Augusta, 2023, kamar yadda jaridar Headtopics ta ruwaito.
Mai shari’a Ahuchaogu a watan Agusta ya jingine yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC da Social Democratic Party (SDP) suka shigar.
Haka nan kuma Alkalin ya tanadi hukunci kan karar da jam’iyyar Labour ta shigar a ranar 26 ga watan Satumba bayan sake sauraren karar kamar yadda kotun daukaka kara ta bada umarni.
Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Yaba da Hukuncin Kotu
A wani rahoton kuma Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna farin cikinsa bisa hukuncin da Kotun zabe ta yanke wanda ya tabbatar masa da nasara.
Uba Sani ya ce hukuncin ya ƙara tabbatar da muradin al'ummar jihar Kaduna da kuma wanda suka damƙa wa amanar mulkinsu.
Asali: Legit.ng