Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Yaba da Hukuncin Kotu Na Tabbatar da Nasararsa
- Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna farin cikinsa bisa hukuncin da Kotun zabe ta yanke wanda ya tabbatar masa da nasara
- Uba Sani ya ce hukuncin ya ƙara tabbatar da muradin al'ummar jihar Kaduna da kuma wanda suka damƙa wa amanar mulkinsu
- Ya kuma yi kira ga abokin adawarsa na PDP, Isa Ashiru Kudan, ya haɗa hannu da shi wajen magance kalubalen Kaduna
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana jin dadinsa kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke ranar Alhamis.
A cewarsa, Kotun ta tabbatar masa da nasarar da ya samu a zaben gwamna wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Gwamna Sani ya nuna farin cikinsa da hukuncin Kotun ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Manhajar X jim kaɗan bayan yanke hukunci.
Ya ce hukuncin da kotu ta yanke ya kara tabbatar da muradin al’ummar jihar Kaduna da kuma nauyin da suka ɗora masa na tafiyar da harkokin shugabanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma Gwamnan ya yaba wa Kotu bisa tsaya wa tsayin daka har ta tabbatar da tsarin demokaraɗiyya na zabe yayin yanke hukunci.
Uba Sani ya aike da saƙo da Isa Ashiru
Bayan haka Malam Uba Sani ya yaba wa abokin hamayyarsa na PDP, Isa Ashiru Kudan bisa matakin da ya ɗauka na zuwa Kotu domin ta share masa hawayensa.
A cewarsa, hakan ya ƙara tabbatar da imaninsa ga tsarin demokuraɗiyya da kuma wayewarsa a fagen siyasa.
Gwamna Sani ya ce:
"Ina kira ga Honorabul Isa Ashiru Kudan da sauran mambobin jam'iyyar adawa PDP su haɗa hannu da mu a yunƙurin da muke na ɗaga martabar Kaduna."
"Ba abu ne da ya shafi mutum ɗaya ba, al'ummarmu na son kowa ya tashi tsaye don magance dimbin kalubalen da ke addabar jihar nan."
"Idan har kan ‘yan siyasa ya haɗu, wata alama da ke nuna cewa neman zaman lafiya, tsaro, da ci gaban jiharmu su ne ginshikin shiga harkokin siyasa."
Wani jigon APC a cikin birnin Kaduna, Zaharadden Aliyu, ya shaida wa Legit Hausa cewa sun yi farin cikin da hukuncin Kotu kan zaben Malam Uba Sani.
Ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya ƙara wayar wa da mutanen Kaduna kai kan waɗanda ya cancanta su zaɓa.
Ya ce:
"Mun san hukuncin da Kotu ta yanke tun farko, amma yan PDP suka yaɗa farfagandar wai za a sake zaɓe. To ita gaskiya guda ɗaya ce kuma komai daren daɗe wa zata fito."
"Mu yanzu a Kaduna Muslim Muslim muke yi, ba wanda zai zo mana da wani sabon tsari, Uba Sani ya ci zaɓe kuma Kotu ta tabbatar, muna fatan duk inda aka je wannan hukuncin ba zai canza ba."
Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Sa Labule da Gwamnoni Sama da 10 a Villa
Kuna da labarin Mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima, na jagorantar taron majalisar NEC yanzu haka a Aso Villa da ke Abuja.
Rahoto ya nuna gwamnonin jihohi da dama sun halarci taron na yau Alhamis karo na uku bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng