INEC Ta Nuna Damuwa Kan Yanayin Tsaro a Jihohin Kogi da Imo Gabanin Zaben Gwamna
- Hukumar INEC ta bayyana damuwa kan halin rashin tsaro a jihohin Kogi da Imo yayin da take shirin gudanar da zaben gwamna a watan Nuwamba, 2023
- Kwamishinan INEC na kasa, Mallam Mohammed Kudu Haruna, ya bukaci a kara inganta harkokin tsaro domin zaben ya tafi cikin nasara
- Ya kuma yi kira ga masu hannu a lamarin su bari a zauna lafiya don jama'a su samu damar kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Owerri, Jihar Imo - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta nuna damuwa matuƙa dangane da yanayin matsalar tsaro a jihohin Kogi da Imo.
Hukumar ta bayyana damuwa kan lamarin ne yayin da take shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni a jihohin guda biyu nan da 'yan watanni.
Kwamishinan INEC na ƙasa, Mallam Mohammed Kudu Haruna, ya nuna bukatar inganta matakan tsaro a Jihohin biyu da kuma Bayelsa domin gudanar da zabe cikin lumana da samun nasara.
Haruna ya bayyana damuwar ne a wurin taron masu ruwa da tsakin midiya na zaben gwamna 2023 a Owerri, babban birnin jihar Imo, ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma yi kira ga dukkan masu hannu a lamarin su bari zaman lafiya ya samu gindin zama domin a bai wa masu kada kuri’a damar sauke nauyin da ke kansu.
Yaushe za a yi zaben gwamnoni a wadannan jihohin?
INEC ta zabi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin ranar gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya, jihar Imo da ke Kudu maso Gabas da kuma jihar Bayelsa.
Tuni jam'iyyun siyasa musamman na sahun gaba APC da PDP da kuma Labour Party suka yi nisa a shirye-shiryen zuwan zaben bayan gudanar da zaben fidda yan takarar da zasu fafata a zabukan.
Sai dai yanayin tsaro na kara tabrabrewa a jihohin musamman jihar Imo, inda ko a makon jiya wasu yan bindiga sun kashe jami'an tsaro akalla 8 tare da kone gawarwakinsu a cikin motoci biyu.
Mutane 6 Sun Mutu a Sabon Harin da Aka Kai Kudancin Jihar Kaduna
A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun yi ajalin mutane shida har da ƙananan yara a sabon harin da suka kai kudancin jihar Kaduna.
Rahoto ya nuna maharan sun shiga kauyen Takanai, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, inda suka buɗe wuta kan jama'a da daren Talata.
Asali: Legit.ng