Akwa Ibom: Gwamnan PDP Ya Hana Jiga-Jigan Jam’iyyar Tatse Baitul Malin Jiharsa

Akwa Ibom: Gwamnan PDP Ya Hana Jiga-Jigan Jam’iyyar Tatse Baitul Malin Jiharsa

  • Gwamna Umo Eno ya gargadi shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da sauran masu fada a ji a jihar Akwa Ibom
  • Gwamna Eno ya ce ba zai ba da kafar da za a sace baitul malin jihar ba domin ya gwammaci shekaru hudu masu kyau fiye da wa'adi biyu mara amfani
  • Ya aike sakon ne ga wasu shugabannin jam'iyyar da masu fada aji da suka sha alwashin janye goyon bayansu daga gare shi idan ya nemi zarcewa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uyo, Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa ya gwammaci shekaru hudu masu kyau da amfani a karagar mulki fiye da wa'adi biyu mara amfani.

Gwamna Eno ya bayyana hakan ne yayin da yake martani da sukar da yake sha daga wasu fusatattun mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wadanda suka sha alwashin janye goyon bayansu daga gare shi idan ya yi kokarin zarcewa a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Shugabanni da Kusoshin Jam'iyya Sun Jingine Tsohon Gwamna, Sun Koma Inuwar APC

Gwamnan Akwa Ibom ya ce ya fi son shekaru hudu masu kyau a mulki
Akwa Ibom: Gwamnan PDP Ya Hana Jiga-Jigan Jam’iyyar Tatse Baitul Malin Jiharsa Hoto: Umo Eno/PDP
Asali: Facebook

An tattaro cewa Gwamna Eno ya toshe duk wata hanya da mambobin jam'iyyar za su bi su tatse baitul malin jihar, wanda hakan ya haddasa zazzafan takaddama tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da gwamnan.

Gwamna Eno, wanda ya yi jawabi ga jama'a a bikin cika shekaru 36 da kafa jihar, ya jaddada cewa a shirye yake ya yi mulki mai tasiri a wa'adinsa na farko maimakon gazawa a wa'adi biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ya ce:

"Ni ajizi ne, amma na yi alkawari cewa ba zan jefa jihar nan cikin wani abu da za mu yi danasani ba da gangan. Za mu yi iya bakin kokarinmu."

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen saka hannun jari a ayyukan da za su kawo sauyi wanda zai yi tasiri ga tattalin arzikin jihar da mazauna cikinta sama da miliyan 7.9.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tashin Hankali Yayin da Wasu 'Yan Bindiga Suka Halaka Jami'an Tsaro A Kan Bakin Aiki

Gwamna Eno ya aika da muhimmin sako ga shugabannin jam’iyya da masu fada a ji

Gwamna Eno ya ce ba zai ba da kai bori ya hau ba saboda matsin lambar wasu yan tsirarun mutane don cutar da mutanen jihar Akwa Ibom.

Ya bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta kulla yarjejeniya da shugabannin kananan hukumomi domin samun fili mai fadin hekta 50 a kowane yanki domin noma.

Matsin rayuwa: Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci malaman Musulunci da su daina la'antar shugabanni

A wani labari na daban, mun ji cewa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya yi kira ga malaman addini a kasar da su guji yin kalaman da ka iya haddasa rikici da barazana ga zaman lafiya a tsakanin Musulmai a kasar.

Ibrahim, wanda ya kasance babban dan jagoran Darika, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a Bauchi daga cikin shirye-shiryen da suke yi na bikin Maulidi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng