Ondo: Sanatan APC Ya Nada Sabbin Hadimai 100, Zai Kowane Mutum Tallafin N300,000
- Sanatan Ondo ta kudu ya naɗa sabbin masu taimaka masa na musamman 100 'yan asalin mazaɓarsa
- Dakta Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa kowane ɗaya daga cikin waɗan nan mutane zai samu tallafin N300,000 a karon farko
- Ya yi wannan naɗe-naɗen ne a yunkurinsa na tabbatar da nagartaccen wakilci ga mutanen da suka zaɓe shi bayan cika kwana 100 a ofis
Jihar Ondo - Sanata mai wakiltar mazaɓar jihar Ondo ta kudu a inuwar jam'iyyar APC, Dakta Jimoh Ibrahim, ya naɗa sabbin mataimaka na kai da kai 100 a mazaɓarsa.
Sanata Ibarahim ya bayyana haka ne a wata sanawar da ya raba wa manema labarai kuma ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter ranar Laraba, 20 ga watan Satumba.
Dakta Ibrahim ya kuma sanar da cewa kowane mutum ɗaya daga cikin mutanen mazaɓarsa 100 da ya naɗa a matsayin masu taimaka masa zai samu tallafin N300,000.
A sanarwan da ya wallafa, Sanatan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yayin da na cika kwanaki 100 a ofis a yau, ina mai farin cikin sanar da nadin wadannan a matsayin mataimakana wajen gudanar da ayyukana na majalisa."
“Waɗan nan mutane 100 da na zaƙulo a mazaɓata za su karbi ƙunshin kuɗi Naira 300,000 kowane mutum ɗaya a matsayin tallafi, sannan kuma za mu kaddamar da gyaran hanyoyi, kariya da gine-gine a mazaɓar mu."
"Wannan naɗe-naɗe na nuna yadda na sadaukar da kaina wajen tabbatar da nagartaccen wakilci, biyan buƙatun al'ummar mazaɓata da taimaka wa manufofin majalisa masu tasiri ga rayuwar mutane."
Yaushe Sanatan zai rantsar da sabbin hadiman?
Haka nan kuma ya bayyana cewa dukkan waɗanda wannan naɗi ya shafa za a rantsar da su ranar 20 ga watan Satumba, 2023 a ɗakin taro na jami'ar Fortune da ke Igbotako.
Kotun Amurka Ta Amince da Bukatar Atiku Kan Takardun Karatun Tinubu
A wani rahoton na daban Kotun Majistire a ƙasar Amurka ta amince da buƙatar Atiku Abubakar na PDP kan takardun karatun Bola Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya roƙi Kotu ta bada umarnin tilasta wa jami'ar sakin dukkan takardun shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng