Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Hadimai 136 a Gwamnatinsa
- Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya amince da naɗa sabbin hadimai 136 a matsayin mambobin majalisar zartarwa
- A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ya ce waɗanda aka naɗa sun fito ne daga kananan hukumomin jihar 17
- Ya ce nan ba da daɗewa ba za a sanar da su muƙamin da aka ba su kuma naɗin zai fara aiki ne nan take
Plateau - Gwamnan jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya, Caleb Mutfwang, ya naɗa nutane 136 a matsayin sabbin mataimaka na musamman, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana haka da daren ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba, 2023 a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Gyang Bere.
Sanarwan ta nuna cewa gwamnan ya kwatanta adalci wajen zakulo hadiman daga sassan kananan hukumomi 17 da ke jihar Filato kuma kowane ƙaramar hukuma ya ɗauki mutum Bakwai.
Sai dai gwamnan bai bayyana muƙaman da ya naɗa sabbin mataimakan ba har kawo yanzu amma sanarwan ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da su aikin da zasu yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kakakin mai girma gwamnan ya bayyana cewa za a sanar da su muƙaman da aka naɗa su a ƙananan hukumominsu nan ba da daɗewa ba, jaridar Gazettengr ta tattaro.
Sunayen wasu daga cikin sabbin hadiman gwamna Mutfwang
A sanarwan, Gyang Bere ya ci gaba da cewa:
"Sabbin masu taimaka wa gwamna na musamman, waɗanda sunayensu ya fito a nan ƙasa su ne rukunin farko, kuma zasu fara aiki ne nan take."
"Wasu daga cikin waɗanda aka naɗa sun haɗa da Honorabul Dalyop Pin, Mis Nyam Jemima, Mis Patience Ufwalal, Dachomo Sunday, Shim Malau, Dabot Dung, Mista Pam Nuhu, Mista Samson Chuwang."
"Sauran sun ƙunshi Aaron Jamo, Gimbia Tahu, Yahaya Ibrahim, Atoyi Daniel, Katuk Ahamdu, Ughili Agaji, Ichi David da Sunday Wada, da dai sauransu."
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan CBN da Mataimakansa 4
A wani rahoton na daban Tinubu ya amince da naɗin Dakta Olayemi Michael Cardoso, a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Shugaban ƙasar ya kuma naɗa mataimakan gwamnan guda huɗu duka na tsawon shekaru 5 idan majalisar dattawa ta tabbatar da su.
Asali: Legit.ng