Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara a Jihar Ribas

Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara a Jihar Ribas

  • Yayin da Kotun zaɓe ke ci gaba da yanke hukunci kan kujerun siyasa, da alamu hukuncin zaɓen gwamnoni na dab da fara fitowa
  • Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben jihar Ribas ta tanadi hukuncin da zata yanke kan karar da ta kalubalanci nasarar gwamna Fubara
  • Tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya halarci zaman amma ya ƙi ce wa yan jarida komai kan shari'ar bayan kammala zama na ƙarshe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rivers - Kotun sauraron kararrakin zaɓen jihar Ribas ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar karkashin inuwar jam'iyyar APC, Tonye Cole, ya shigar.

Mista Cole na kalubalantar nasarar gwamna Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP a zaben da ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Gwamna Fubara na jihar Ribas da ɗan takarar APC.
Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara a Jihar Ribas Hoto: channelstv
Asali: UGC

Kwamitin alkalai uku da suka saurari ƙarar a Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Cletus Emifonye, ya ɗage zaman zuwa ranar yanke hukunci, wanda za a sanar daga baya.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP, Ta Yi Fatali Da Karar Yan Takarar APC Da LP

Kotun ta jingine yanke hukunci ne bayan karban bayanan rufe shari'a a rubuce daga kowane ɓangare da kuma gabatar da ƙorafe-korafen da ke cikin ƙarar baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Abuja ya halarci zaman Kotu

Baya ga ɗan takarar jam'iyyar APC, Cole, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya halarci zaman ƙarshe da aka yi a Kotun.

Wike, babban jigon jam'iyyar PDP wanda ya sauka ya miƙa wa Fubara, ya yi wa Bola Tinubu aiki a zaben shugaban ƙasa na watan Fabrairu, 2023.

Sai dai tsohon gwamnan bai yarda ya yi hira da manema labarai ba dangane da abubuwan da aka tattauna a ranar bayan kammala zaman Kotun, The Nation ta tattaro.

Mista Cole na APC ya gabatar da shaidu 40 a gaban Alkalan domin tabbatar da ikirarinsa cewa Fubara bai cancanci shiga zaben gwamna ba a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Rasa Kujerun Sanata 2 a Jiha Ɗaya, Kotun NASS Ta Yanke Hukunci

Jam'iyyar APC Ta Fara Rijistar Mambobinta Miliyan 40 Ta Intanet

A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC ta fara shirin tunkarar babban zaben 2023, ta ce aiki ya yi nisa na yi wa mutane sama da miliyan 40 rijista ta Intanet.

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya koka kan adadin yawan kuri'un da Tinubu ya samu a zaben shugaban ƙasa 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262