Kira 1 Atiku Zai Yi Wa Bola Tinubu Ya Kori Wike A Mukaminsa Na Minista
- Jigon PDP, Daniel Bwala ya ce Atiku na kiran Tinubu da bukatar korar Wike ko gama waya ba za su yi ba zai fatattake shi
- Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Arise a yau Laraba 13 ga watan Satumba a Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi ikirarin korar Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya ce kiran waya daya daga Atiku ya isa a kori Nyesom Wike a mukaminsa.
Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da Arise TV a yau Laraba 13 ga watan Satumba, Legit ta tattaro.
Meye Bwala ya ce kan Atiku da Wike?
Ya ce idan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kira Shugaba Tinubu zai iya korar ministan Abuja, Nyesom Wike.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan na zuwa ne bayan Wike ya yi barazanar korar Atiku Abubakar daga jam'iyya PDP.
Ya ce:
"Kwanakin nan, har ya na da karfin gwiwar cewa zai kori dan takarar jam'iyyar PDP.
"Lokacin da Atiku su ka kirkiri jamiyyar PDP da wasu, ina ya ke? Ya na aiki da kungiyar sufuri a Port Harcourt.
"Bari na fada maka, idan Atiku ya kira Tinubu kan ya kori Wike, kafin su gama waya kore shi.
"Wannan ya na nuna yadda Tinubu ya ke mutunta Atiku da karrama shi."
Wike ya yi ikirarin korar Atiku a PDP
Wike wanda yanzu shi ne ministan birnin Tarayya, Abuja a gwamnatin APC ya kasance dan jam'iyyar PDP.
Wannan lamari ya jawo cece-kuce a bangarori da dama inda wasu ke kiran a kore shi daga jam'iyyar PDP saboda zagon kasa.
Jam'iyyar PDP na zargin Wike da yi wa APC aiki a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu.
Wike ya yi barazanar korar Atiku daga PDP
A wani labarin, ministan birnin Tarayya, Abuja Nyesom Wike ya yi barazanar korar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar daga jam'iyyar.
Wike ya kasance dan jam'iyyar PDP da ke da mukami a gwamnatin APC ta Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng