Jerin Sanatocin APC 4 Da Kotun Zabe Ta Tsige Da Kuma Dalili

Jerin Sanatocin APC 4 Da Kotun Zabe Ta Tsige Da Kuma Dalili

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawa a zaben majalisar dokokin tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kasancewarta jam'iyyar da ta fi yawan sanatoci a zauren majalisar dattawan, APC ta karbe mukaman shugabanci a majalisar.

Sanatocin APC da aka tsige
Jerin Sanatocin APC Da Aka Tsige Cikin Kwanaki 100 a Ofis Da Dalili Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

APC na hanyar rasa kujeru da yawa a majalisar dattawa

Sai dai kuma, alamu sun nuna jam'iyyar na gab da rasa matsayinta a matsayin jam'iyya mafi rinjaye a majalisar dokokin tarayyar, musamman a majalisar dattawa.

Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisun dokokin tarayya ta tsige wasu sanatoci da aka zaba a inuwar jam'iyyar a baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalla hudu daga cikinsu ne suka rasa kujerunsu cikin kwanaki 100 a ofis.

Kara karanta wannan

PDP Na Kara Shanyewa Yayin da Kotun Zabe Ta Tsige Sanata 1 Da Yan Majalisar Wakilai 3

Imma dai kotun ta ayyana abokan hamayya a matsayin wadanda suka lashe zaben ko ta yi umurnin sake zabe.

Ga jerin sanatocin APC da kotun zabe ta tsige cikin kwanaki 100 a ofis:

1. Sanata Thomas Onowakpo, Delta ta Kudu

A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne kotun zabe da ke zaune a jihar Delta ta tsige dan majalisar tarayya na APC sannan ta yi umurnin sake sabon zabe cikin kwana 90.

Hukuncin kotun ya biyo bayan wata kara da Michael Diden, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shigar.

Diden ya nemi a soke zaben Onowakpo kan zargin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kin bin tsari wajen sanar da sakamakon.

2. Jibrin Isah, Kogi ta Gabas

Kotun zabe da ke zama a Lokoja, babban birnin jihar Kogi ta kuma tsige dan majalisar tarayya na APC a ranar Talata, 5 ga watan Satumba.

Kotun ta umurci INEC da ta gudanar da zaben cike gurbi a yankin.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya

Dan takarar PDP ya tunkari kotun kan soke zaben a rumfunan zabe 94 da kuri'u sama da 59,730.

Za a yi zaben cike gurbin ne a rumfunan zaben da abun ya shafa.

3. Abubakar Sadiku-Ohere, Kogi ta tsakiya

Mai shari'a Kemakolam Ojiako na kotun zabe da ke zama a jihar Kogi ya tsige Sadiku-Ohere sannan ya ayyana Natasha Akpoti-Uduaghana matsayin wacce ta lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a yankin.

A karar da ta shigar gaban kotun zaben, Natasha ta nemi a soke nsarar Sadiku-Ohere sannan ta nemi kotu ta sanar da ita a matsayin wacce ta lashe zaben.

4. Emmanuel Udende, Benue ta Arewa Maso Gabas

A ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba, kotun sauraron korafe-korafen zaben yan majalisun tarayya da ke zama a Makurdi, babban birnin jihar Benue ta tsige sanatan na APC.

Ta ayyana Gabriel Suswam, dan takarar PDP kuma tsohon gwamnan jihar a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Ga ci ga rashi: An kwace kujerar sanatan PDP a Arewa, an ba wani fitaccen tsohon gwamnan APC

Dan majalisar tarayya na PDP da kotu ta tsige ya sha alwashin kalubalantar hukuncin

A wani labarin, mun ji cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas daga Filato, Dachung Musa Bagos, ya yi martani kan hukuncin kotun zabe da ta tsige shi daga kujerarsa.

Bagos wanda ya kasance dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sha alwashin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke a kan zabensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng