Majalisar Dokokin Ogun Ta Karbi Sunayen Kwamishinoni 10 da Gwamna Ya Nada
- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tura ƙarin sunayen mutum 10 da ya naɗa kwamishinoni zuwa majalisar dokoki
- Majalisar ta tabbatar da zuwan sunayen, kuma ta fara shirye-shiryen fara tantance su ranar Laraba, 13 ga watan Satumba
- Tun bayan rantsar da shi, gwamna Abiodun ya aika sunayen kwamishinoni 8 zuwa majalisa kuma har yau bai rantsar da su ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Majalisar dokokin jihar Ogun ta karɓi jerin sunayen ƙarin kwamishinoni 10 daga mai girma gwamna Dapo Abiodun na jam'iyyar APC.
Magatakardan majalisar, Mista Deji Adeyemo, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Sanarwan ta nuna cewa mambobin majalisar dokokin za su fara aikin tantance mutanen da gwamnan ya naɗa ranar Laraba (Yau) 13 ga watan Satumba, 2023 daga ƙarfe 2:00 na rana zuwa abinda ya sawwaƙa.
Jerin sunayen sabbin kwamishinon da za a tantance
Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen sabbin kwamishinonin da majalisar zata tantance, ga su kamar haka;:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Honorabul Adeleye-Oladapo Adijat
2. Injiniya Taiwo Oludotun
3. Mista Sofela Adebola Emmanuel
4. Honorabul Ilori-Oduntan Olufemi
5. Injiniya Dairo Oluwagbenga
6. Honorabul Owootomo Bolu
7. Mista Oresanya Oladimeji
8. Honorabul Balogun Ademola
9. Mista Osunbiyi Tunde
10. Mista Fagbayi Sesan.
Bugu da ƙari, sanarwan ta umarci waɗanda aka naɗa su kai kwafin takardun karatunsu da sauran bayanansu ga ofishin magatakardan majalisa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Laraba.
Kwamishinoni na wa gwamnan ya naɗa zuwa yanzu?
Jaridar PM News ta tattaro cewa gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya naɗa kwamishinoni 8 ne kacal tun bayan karɓan rantsuwar kama aiki a zango na biyu.
Idan baku manta ba, a watan Yuli, 2023 gwamnan ya tura sunayen kwamishinoni Takwas ga majalisar dokokin kuma tuni aka tantance su amma har yanzu ba a rantsar da su ba.
Adamawa: Ban Taba Aje Biliyan Daya a Asusun Banki Ba a Matsayin Gwamna, Ngilari
A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Adamawa ya tabbatar da cewa bai taɓa samun kuɗin da suka kai Naira biliyan ɗaya ba a asusunsa har ya gama mulki.
A kwanakin bayan an ji Bala Ngilari na cewa zai iya faɗuwa ya suma idan ya ga kuɗi Biliyan N1bn a cikin asusun bankinsa.
Asali: Legit.ng