Dan Majalisar Tarayya Na PDP Da Kotu Ta Tsige Ya Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin
- Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas, Dachung Musa Bagos, ya magantu a kan hukuncin kotun zabe da ta tsige shi
- Musa Bagos ya ce sam bai gamsu da hukuncin ba inda ya sha alwashin zuwa kotun gaba domin daukaka kara
- A cewarsa, kotun zaben ta yanke hukunci a kan abun da ya shafi kafin zabe wanda bata da hurumi a kansa
Jihar Plateau - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas daga Filato, Dachung Musa Bagos, ya yi martani kan hukuncin kotun zabe da ta tsige shi daga kujerarsa.
Bagos wanda ya kasance dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sha alwashin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke a kan zabensa.
"Zan daukaka kara a kan hukuncin kotun zabe", dan majalisar tarayya na PDP
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, dan majalisar ya yi watsi da hukuncin, cewa ya saba doka, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi korafi cewa abubuwan da kotun zaben ta duba wajen zartar da hukunci lamari ne na kafin zabe wanda bata da hurumi a kansa.
Ya ce:
"Akwai alamun tambaya sosai a sakamakon hukuncin da kotun zaben ta yanke wanda ya saba muradin mutanen mazabar Jos ta kudu da Jos ta arewa, shin nasarar da aka samu da sama da kuri'u 95,000 bisa 31,000 zai iya zama lamari na ilimi kawai? Ya nuna karara cewa muradan mutane ba su da mahimmanci saboda dalilai na kashin kai da ba su da tushe.
"Hukuce-hukuncen kotun zabe na baya ya riki cewa mambobin jam'iyya ko jam'iyya da kanta ne kawai suke da hurumin kalubalantar zabar ko daukar nauyin dan takara. Bugu da kari, irin wannan batutuwa lamari ne na kafin zabe, na yi mamakin dalilin da ya sa wannan kwamitin yake tunani daban."
Bagos ya yi kira ga mazabarsa da mabiya jam'iyyar da su kwantar da hankalinsu tare da jajircewa yayin da yake neman hakkinsa a kotun daukaka kara, rahoton Vanguard.
Kotu Ta Soke Zaben Dan Majlisar PDP Na 3 a Jihar Plateau
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a Jos, babban birnin jihar Plateau, ta soke zaɓen ɗan majalisar wakilai, Dachung Musa Bagos.
Bagos, wanda yake wakiltar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a majalisar wakilai an zaɓe shi ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Asali: Legit.ng