Zaben Gwamnan Jihar Imo Na 2023: Primate Ayodele Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara
- Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi hasashen yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Imo zai kasance
- Ya yi hasashen cewa Gwamna Hope Uzodimma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ne zai lashe zaben
- Primate Ayodele ya ce APC ta shirya ma zaben fiye da sauran jam'iyyun adawa
Jihar Imo - Gabannin zaben gwamna mai zuwa a jihar Imo, shahararren malamin addini Primate Elijah Ayodele ya yi hasashe kan wanda zai lashe zaben.
Za a yi zaben gwamnan jihar Imo a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta tsara.
Za a gwabza a zaben tsakanin manyan jam'iyyun siyasa uku wato Peoples Democratic Party (PDP), the Labour Party (LP) da All Progressives Congress (APC).
Da yake bayyana matsayinsa kan zaben mai zuwa, Primate Ayodele ya je shafinsa na soshiyal midiya a dandalin X, yana mai bayyana cewa ya hango APC a saman sauran jam'iyyun siyasa a zaben.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya rubuta:
"Na hango cewa zaben gwamna da ke tafe a jihar Imo nasara zai zama a bangaren jam'iyyar All Progressive Congress, domin a shirye suke sosai don samun nasara fiye da kowace jam'iyyar siyasa."
Zaben Imo: Dalilin da yasa Uzodimma na APC zai yi nasara - Primate Ayodele
A wani bidiyo da ya biyo rubutun nasa, ya bayyana cewa APC ta fi shirya ma zaben foye da yan adawa.
Ya ce APC ba za ta yi nasara ba idan gwamna mai ci Hope Uzodimma, ya gaji da kujerar shugabancin.
A halin da ake ciki, Gwamna Uzodimma zai kara da Sanata Samuel Anyanwu na jam'iyyar PDP da Cif Ukaegbu Ikechukwu Joseph na jam'iyyar Labour Party.
Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya
Gwamnan Akwa Ibom ya sanya dokar kulle a wasu kauyuka 4 na jihar
A wani labarin kuma, Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers a ranar Talata ya sanya dokar kulle a ƙauyukan Ugaga, Igbekurekor, Benekaba da Ijama na ƙaramar hukumar Yala ta jihar.
Gwamnan ya sanya dokar kullen ne bayan an samu ɓarkewar rikici a ƙauyukan, cewar rahoton PM News.
Rikicin filaye da iyakoki a tsakanin ƙauyukan guda huɗu ya jawo matsalar rashin tsaro a yankin wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Asali: Legit.ng