Fasto Ayodele Ya Lissafo Gwamnoni 4 Da Kotu Ba Zata Soke Nasararsu Ba

Fasto Ayodele Ya Lissafo Gwamnoni 4 Da Kotu Ba Zata Soke Nasararsu Ba

  • Fasto Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa wasu gwamnonin kotu ba za ta ƙwace nasararsu ba
  • Babban faston a wani rubutu da ya yi a Twitter, ya lissafo gwamnoni huɗu na jam'iyyun PDP, APC da Labour Party
  • Idan za a tuna dai kotunan zaɓe a jihohi 25 masu sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna sun tanadi hukuncinsu wanda za su zartar a ƙarshen watan Satumba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Fasto Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya yi hasashen cewa ba kotun zaɓen da za ta soke zaɓen gwamnoni huɗu a Najeriya.

Jerin sunayen gwamnonin da Ayodele ya hango sun haɗa da na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), All Progressives Congress (APC) da Labour Party.

Fasto Ayodele ya lissafo gwamnonin da ba za a soke zabensu ba
Fasto Ayodele ya yi hasashen makomar Agbu Kefas, Sanwo-Olu, Umo Eno a kotu Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Kefas Agbu
Asali: Twitter

A cewar The Punch, kotunan da ke zama a jihohi 25 cikin 28 da aka gudanar da zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris, ka iya yanke hukuncinsu kafin ƙarshen watan Satumba, domin da yawa daga cikinsu sun tanadi hukuncinsu.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Atiku, Peter Obi Za Su Tarar a Kotun Koli

Amma a cikin sabon hasashen da ya fitar a Twitter, Ayodele ya bayyana cewa babu kotun da za ta soke zaɓen gwamnoni huɗu, duk kuwa da irin abubuwan da abokan takararsu suka bayyana a gaban kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ayodele ya yi hasashen makomar Kefas, Sanwo-Olu, Oti, Mbah, da Eno

A cewar babban faston kotu ba za ta iya ƙwace nasarar Agbu Kefas, gwamnan PDP na jihar Taraba, Alex Otti na jam'iyyar Labour Party a jihar Abia.

Fasto Ayodele ya kuma bayyana cewa da wuya a iya ƙwace nasarar gwamnan jihar Enugu na jam'iyyar PDP, Peter Mbah, idan gwamnan ya koma ga ubangiji.

Babban malamin addinin ya kuma ƙara da cewa bai ga wanda zai ƙwace nasarar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ba, duk kuwa da irin abin da masu shigar da ƙara suka gabatar a kotu.

Kara karanta wannan

Hadimai 2 Na Gwamnan PDP da Wasu Manyan Jiga-Jigai Sun Koma APC Ana Dab Da Sabon Zaɓe

Ayodele ya kuma bayyana cewa kotu ba za ta soke zaɓen gwamnan PDP Umo Eno na jihar Akwa Ibom ba.

Kotu Ta Soke Zaben Beni Lar

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a jihar Plateau, ta soke zaɓen ƴar majalisar jam'iyyar PDP, Beni Lar.

Kotun ta kuma tabbatar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Vincent Bulus a matsayin halstaccen wanda ya lashe zaɓen na mazaɓar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kuɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel