Wike Na Son Fitowa Takarar Shugaban Kasa a 2027, In Ji Na Hannun Daman Atiku Abubakar

Wike Na Son Fitowa Takarar Shugaban Kasa a 2027, In Ji Na Hannun Daman Atiku Abubakar

  • An bayyana ainihin dalilin da ya sa Wike yake ta ƙoƙarin faɗa da wasu manyan jam'iyyar PDP
  • Daya daga cikin jiga-jigan yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Don Pedro Obaseki, ya ce so yake ya kawo rikici sai daga baya ya nemi takara
  • Obaseki ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da Wike ya yi kira da a dakatar da Atiku da Aminu Tambuwal

FCT, Abuja - A yanzu haka dai rikicin cikin gida na ta ƙara ruruwa a cikin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato jam'iyyar PDP.

Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya nemi a dakatar da ɗan takarar shugabancin ƙasa Atiku Abubakar, da kuma tsohon gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal daga jam'iyyar.

Na hannun daman Atiku ya tona asirin Nyesom Wike
Na hannun daman Atiku ya ce takarar shugabancin ƙasa Wike yake son fitowa a PDP. Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Obaseki ya ce Wike takarar shugaban ƙasa yake son yi

Sai dai ɗaya daga cikin jiga-jigan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata Don Pedro Obaseki, ya bayyana cewa Wike yana son raunana jam'iyyar ne ta yadda zai yi takara cikin sauƙi a 2027 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mu ba Sakarkaru ba ne: Abin da Ya sa Wike Ya Dage Sai Ya Karya PDP - Mutumin Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obaseki ya ƙara da cewa Wike ba kowa ba ne, kuma ya yaudari jam'iyyar ta PDP bayan kai wa ga matakin nasarar da ya samu da taimakonta kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Obaseki ya bayyana hakan ne ranar Litinin a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, inda yake yi wa Wike martani kan kalaman da ya yi na baya-bayan nan.

Ya kuma ce da alama babban burin Wike shi ne neman takarar shugabancin ƙasa a 2027, wanda a dalilin hakan ne yake kokarin yaƙar duk waɗanda za su iya ba shi matsala.

Nyesom Wike zai gyara tituna 135 a Abuja

A wani rahoto da Legit Hausa ta kawo a baya, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya kaddamar da aikin gyaran tituna 135 da ke cikin birnin na Abuja.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici Ya Kunno a Jam'iyyar PDP, Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Ƙara Hargitsa Jam'iyyar

Hakan dai na zuwa ne bayan shafe kwanaki da Wike ya yi a matsayinsa na minista, inda ya sha alwashin yin gyare-gyaren da za su inganta rayuwar mazauna birnin.

Wike ya musanta batun gayyato EFCC da ICPC don bincikar magabacinsa

Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan musanta batun gayyato EFCC da ICPC da aka ce ministan birnin tarayya Nyesom Wike ya yi domin su binciki ayyukan da tsohon ministan Abuja ya yi.

Sai dai an bayyana cewa akwai wasu ayyuka da dama da aka yi wanda Wike bai gamsu da su ba, amma kuma bai nemi EFCC ko ICPC su zo don gudanar da bincike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng