"Ku Ja Kunnen Wike" Tsagin Atiku Ya Maida Martani, Ya Aike da Sako Ga PDP

"Ku Ja Kunnen Wike" Tsagin Atiku Ya Maida Martani, Ya Aike da Sako Ga PDP

  • Rigingimun cikin gida da suka addabi babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ya ɗauki sabon salo
  • Tsagin tawagar G5 ƙarƙashin tsohon gwamnan Ribas, Nyeson Wike, ya yi kira da a dakatar da Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal
  • A ɗaya bangaren, tsagin Atiku ya buƙaci shugabannin PDP su ja wa Wike kunne ya dawo kan hanya domin kada ya zama butulu

FCT Abuja - Rikicin jam'iyyar PDP na neman dawowa ɗanye yayin da tsagin ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya maida martani kan kiraye-kirayen a dakatar da shi.

Tsagin Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi tir da wannan kira na a dakatar da Wazirin Adamawa daga PDP.

Atiku Abubakar da Ministan Abuja.
"Ku Ja Kunnen Wike" Tsagin Atiku Ya Maida Martani, Ya Aike da Sako Ga PDP Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Sun bayyana bukatar dakatar da Atiku wanda ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya nema a matsayin "mara tushe kuma ta saɓa wa hankali".

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Wike Ke Son Kawo Ruɗani a Jam'iyyar PDP

Jaridar Guardian, ranar Litinin 11 ga watan Satumba, 2023, ta rahoto cewa fafutukar neman dakatar da Atiku ta fara samun karɓuwa a tsakanin manyan jagororin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce Wike ya fara samun haɗin kan wasu mambobin kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) da nufin karɓe ragamar yanke hukunci a jam'iyyar.

Daily Trust ta ce a makon da ya shige ne Wike, ya yi kira ga shugabannin PDP na ƙasa su dakatar da Atiku Abubakar bisa abin da ya kira, "Rashin daidaiton siyasar Atiku."

Manyan kusoshin PDP sun maida martani kan bukatar Wike

Da yake maida martani, babban ƙusa a jam'iyyar PDP wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce Wike na ƙara ƙarfi daga goyon bayan da yake samu a cikin PDP, musamman mambobin NWC.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin kwamitin NWC na aiki da Wike domin faɗaɗa shirinsa da kuma fusata Atiku da waɗanda ke tare da shi.

Tsagin Atiku maida martani ga Wike

Da yake martani kan kiran Wike ranar Litinin, Darektan sashin dabaru na kwamitin kamfen Atiku, Pedro Obaseki ya ce ya zama tilas PDP, "Ta dawo da Wike kan hanya."

Niger: Ɗan Minista Ya Rasa Kujerarsa Ta Dan Majalisar Tarayya a Kotu

A wani rahoton na daban Kotun zaɓe mai zama a jihar Neja ta rushe nasarar ɗan tsohon Ministan yaɗa labarai wanda ya ci zaben ɗan majalisar tarayya

Kwamitin alƙalan Kotun sun soke sakamakon wasu rumfunan zaɓe kana suka umarci INEC ta shirya sabon zaɓe don tantance wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262