Kotun Zabe Ta Soke Nasarar Dan Majalisar PDP a Jihar Plateau

Kotun Zabe Ta Soke Nasarar Dan Majalisar PDP a Jihar Plateau

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar Plateau ta soke nasarar da Peter Gyengdeng ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023
  • An soke nasarar Gyengdeng na jam'iyyar PDP ne bayan kotun zaɓen ta zartar da hukuncinta a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba
  • Bayan hukuncin kotun zaɓen, Fom Chollom na jam'iyyar Labour Party, shi ne ya zama halastaccen ɗan majalisar da zai wakilci Barkin/Riyom a majalisar wakilai

Jos, jihar Plateau - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a birnin Jos, jihar Plateau, ta soke nasarar da Peter Gyengdeng, ya samu a zaɓen ɗan majalisar da ke wakiltar Barkin/Riyom a majalisar wakilai.

Kotun a hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, ta bayyana Fom Chollom na jam'iyyar Labour Party (LP) a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar Barkin/Riyom.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP a Jihar Arewa, Ta Yi Fatali Da Karar Dan Takarar APC

Kotu ta ba Fom Chollom nasara
Kotu ta tabbatar da Fom Chollom a matsayin halastaccen dan majalisar Barkin/Riyom Hoto: Engr. Fom Dalyop Chollom - Sanchos
Asali: Facebook

Jaridar The PUNCH ta rahoto cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Peter Gyengdeng na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaɓen wanda aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.

Fom ya garzaya kotu

Amma Fom sai ya garzaya kotun zaɓe, domin ƙalubalantar nasarar ɗan takarar jam'iyyar PDP bisa dalilin cewa ba jam'iyyar ba ce ta ba shi takara ba, inda ya yi iƙirarin cewa a lokacin da aka ba shi takara, jam'iyyar ba ta tsayayyen shugabanci a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun don hakan sai ta tabbatar da Fom a matsayin halastaccen ɗan majalisar da ya lashe zaɓen, a cikin hukuncin da ta yanke.

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP

A wani labarin na daban kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a birnin Makurdi na jihar Benue ta tabbatar da nasarar sanatan jam'iyyar PDP mao wakiltar Benue ta Kudu, Sanata Abba.Moro.

Kotun ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daniel Onjeh, ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da Abba Moro ya samu a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng