Idan Na Ga Naira Biliyan 1 Sai Na Sume Inji Tsohon Gwamna da Ya Je Kurkuku a Kan Sata

Idan Na Ga Naira Biliyan 1 Sai Na Sume Inji Tsohon Gwamna da Ya Je Kurkuku a Kan Sata

  • James Bala Ngilari ya yi karin haske a kan zargin da ake yi masa na taba dukiyar baitul-mali
  • Da aka zanta da ‘dan siyasar, ya bayyana cewa idan zai ci karo da N1bn a yau, sai ya fadi sumamme
  • Barista Bala Ngilari ya bada labarin tsayawarsa takarar Sanata, aka raina N100, 000 da zai raba

Adamawa - James Bala Ngilari ya ce zai sume idan ya yi ido da ido da Naira biliyan 1, ya nuna bai da kudin da ake zarginsa da mallaka.

A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels a karshen makon nan, Barista James Bala Ngilari ya yi kokarin wanke kan shi daga zargi.

Bala Ngilari wanda ya yi gwamna na watanni a jihar Adamawa tsakanin 2014 da 2015 ya shiga gidan yari a dalilin zargin satar N166m.

Kara karanta wannan

Yadda Binciken Da Tinubu Yake Yi Zai Tona Barnar da Buhari Ya Yi – Kanal Dangiwa

Tsohon Gwamnan Adamawa
Tsohon Gwamnan Adamawa, James Bala Ngilari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

"Zan sume idan na ga N1bn" - Ngilari

Da ake hira da shi a shirin siyasa na ‘Politics Today’, an tambaye shi ko ya mallaki biliyan, ya ce idan har ya ga N1bn, sai ya sume a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar ya bayyana kan shi a matsayin mutum mai gaskiya wanda yake son ayi daidai, yake cewa yin haka ya tara masa dinbin makiya.

"Har gobe zan fada ba tare da tsoro ko alfarma ba, idan aka dauki shari’ar da aka yi da ni bisa zargi biyar a kotu, babu daya da aka yi maganar na karkatar da Naira guda, babu.
Asali ma, na yi yunkurin tsayawa takarar Sanata a APC. Na zagaya, kwanaki biyu zuwa uku kafin zaben tsaida gwani, na tuntubi mutane na ta hannun darektan kamfe da jagorori na.

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa da Ministoci 4 da Su ka Jawo Rudani a Cikin Kwana 15 a Ofis

Masu zaben ‘dan takara su ka fada mani, ‘Ran ka ya dade, idan aka zo maganar wanda ya dace, kai ne ka cancanta, amma gaskiya ba za mu karbi N100, 000 da za ka ba mu ba.

-

Ngilari bai samu tikitin Sanata ba

Daily Trust ta rahoto Bala Ngilari ya na cewa tunaninsa shi ne ya raba N100, 000 ga mutane 200 domin su kama wata sana’a a garuruwansu.

Bisa dukkan alamu ‘yan siyasar sun raina wadannan kudi, su ka tsaida wani ‘dan takaran na dabam.

Wike a kan shari'ar zaben 2023

Nyesom Wike ya ce abin da shari’ar zaben 2023 ta kunsa dabam da hayaniyar dandalin sada zumunta da magoya bayan 'yan siyasa su ke yi.

Duk da ya na ‘dan jam’iyyar PDP, Ministan birnin na Abuja ya karbi mukami a hannun gwamnatin APC kuma ya na goyon bayan Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng